Connect with us

Uncategorized

Za a fara Tsarafa Manja a Jihar Zamfara – Matawalle

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Gwamnan Jihar Zamfara, Bello Matawalle ya sanar da cewa jihar zata fara tsarafa manja a Zamfara.

Naija News Hausa ta gane rahoton ne bisa bayanin da Matawalle ya shaidawa manema labaru a ranar Alhamis a Gusau cewa gwamnatin jihar za ta zuba jari ta kwarai da gaske ga aikin gona tare da kulawa ta musamman ga tsarafa manja.

Ya ce “Za mu hada hannu tare da abokan kasashen waje don gabatar da itatuwan kwakwa don tsarafa manja a jihar.

Ya kara da cewa jihar zata sake farfado da aikin noma don inganta shi hakan a Zamfara.

“Za mu zuba jarurruka sosai ga hidimar gona a yankunan jihar don taimaka wa al’ummomin karkara don sake dawowa da mummunar asarar da suka sha sakamakon ayyukan da hare-haren ‘yan hari da makami ke kaiwa, da kuma korar su daga gonakin su” inji shi.

“Gwamnatin jihar zata sake farfado da hidimar ban ruwa ga Bakalori don karfafa da kuma yaduwar hatsi a duk shekara a Jihar. zamu kuma kadamar da ayuka da zasu farfado da samar da wutan lantarki a kamfanonin mu” inji  Matawalle.

Mun ruwaito a baya a Naija News Hausa cewa Hatsi na kimanin kudi Miliyan daya (N1m) ta kame da wuta a Jihar Jigawa.