Connect with us

Uncategorized

#EidFitr: Dalilin da yasa Gwamna Aminu Masari ya ziyarci Sarkin Daura

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Gwamnan Jihar Katsina, Alhaji Aminu Bello Masari, a ranar Lahadi, 2 da watan Yuni da ta gabata ya kai ziyara ga sarkin Daura, Alhaji Farouk Umar, a nan fadar sa.

Bisa ganewar Naija News Hausa, Gwamna Masari ya ziyarci fadar sarkin ne tare da goyon bayan mataimakin sa, Alhaji Munnir Yakubu.

Gwamnan ya ziyarci fadar sarkin ne a missalin karfe Shida (6:20pm) na maraicen ranar Lahadi, a hakan ne kuma suka bude baki don shan ruwa tare da sarkin, a fadar sa daidai karfe bakwai na maraicen ranar.

An bayyana da cewa Gwamnan ya bukaci addu’ar zaman lafiyar, ci gaba da zamantakewar kwarai a Jihar da kuma kasar gaba daya daga Sarkin Daura.

Naija News Hausa ta fahimta cewa ziyarar Gwamna Masari a lokacin Ramadan a fadar sarkin Daura ya zan kamar al’ada, a yayin da kowace shekara tun shigar sa jagorancin Jihar a shekarar 2015, ya kan ziyarci fadar a lokaci kamar haka.

KARANTA WANNAN KUMA; Za a fara Tsarafa Manja a Jihar Zamfara – Matawalle