Connect with us

Uncategorized

Karshen Duniya! An Jefa wani Mutumi a Kurkuku da laifin kwanci da yaro na miji mai shekaru 10

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Jami’an tsaro sun kame wani a Jihar Katsina mai suna Hassan Garba da ke da shekaru 38 ga haifuwa

An bayyana cewa Jami’an tsaron ‘yan sandan Jihar sun kame Hassan Garba ne da zargin yin jima’i da wani dan yaro mai shekaru goma (10) ga haifuwa.

A halin yanzu bisa ganewar Naija News Hausa, Jami’an tsaro sun riga sun jefa Garba a gidan yari har sai an gama karar shi.

Garba bisa bincike mazauni ne na shiyar Sabuwar Unguwar Quarter, Katsina, an kuma kame shi ne da laifin kwanci da namiji kamar sa, musanman yaro mai shekaru goma da haifuwa.

Ka tuna mun ruwaito a Naija News Hausa a baya cewa An kama wani Malamin Makarantar Almajirai, Malam Murtala Mode da laifin yin Jima’i da daliban sa.

Bisa bayanin da aka bayar ga manema labarai, wani jami’in tsaro mai suna Aliyu Mamman, da ke a karkashin Ofishin ‘yan sanda na Central Police Station, a gefen Kasuwa na Katsina ne ya kame Garba a cikin aikata mugun halin.

An bayyana cewa yaron da Garba yayi jima’i da shi kan kwanta ne a barandan wata gida da ke a garejin Motoci na Mangal kowace rana, anan ne Garba ya ci zarafin yaron da sashi kwanci da shi dole.

Wani jami’in tsaro da ya bukaci kada a bayyana sunansa saboda ba a bashi daman bayani ba, ya ce “Garba kan ziyarci yaron ne a idan yaron ke kwanci anan gaban garejin”

“A rashin sani da ganewar yaron, Garba ya cinma yaron ne a inda yake kwance, ya kuma cire cikin masa wandon sa, anan ya yi jima’i da shi.”

Jami’an Tsaro sun bayyana da cewa sun kame Garba tun ranar 15 ga watan Mayu da ya gabata, akan cewa ya karya dokar kasa ta shafin doka dake a fallen dokoki ta 284  a Arewacin kasar Najeriya.

Mai jagoran kara na Jami’an tsaro, Sergeant Lawal Bello, ya bayyana cewa har yanzu ana kan bincike game da al’amarin, a yayin da Garba ke kurkuku.

Ya karshe da cewa Kotun Karar, a jagorancin Alkali Hajiya Fadile Dikko ta riga ta jefa Garba a kurkuku, anan ne kuma zai kasance har ranar 8 ga watan Yuli 2019, kamin a ci gaba da karar sa.