Connect with us

Labaran Najeriya

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Litini, 3 ga Watan Yuni, Shekara ta 2019

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00
Manyan Labaran Jaridun Najeriya a Yau

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Litini, 3 ga Watan Yuni, 2019

1. Aisha Buhari ta kalubalancin shugabancin kasa

Matar shugaba Muhammadu Buhari, Hajiya Aisha Buhari, ta bukaci hukumar Tsarin Zuba Jarurruka na Ƙasa (N-SIP) da taimaka wa matalauta da ragaggu a Jihar Katsina.

Naija News Hausa na da fahimtar cewa Hajiya Aisha ta bukaci hakan ne don tallafa wa mutanen da mahara da makami suka yi wa barna harma da korar su daga wajen zaman su.

2. CAN ta gayawa Buhari abin da zai yi da zancen Obasanjo game da mayar da Najeriya kasar Musulunci

Hadadiyar Kungiyar Kiristocin Kasar Najeriya (CAN), ta gargadi shugaba Muhammadu Buhari da gwamnatin sa da yin la’akari da bayanin tsohon shugaban kasar Najeriya, Olusegun Obasanjo, game da zancen mayar da kasar Najeriya a matsayin kasar Fulani da musulunci.

Naija News ta samun gana da wannan bayanin shugaban kungiyar CAN, Rev. Dr. Samson Ayokunle, a wata gabatarwa da ya bayar a ranar Asabar da ta gabata da aka bayar ga digan labaran mu.

3. Yadda zaben Gidan Majalisa ya kawo jinkiri ga tsige Oshiomhole

An bayyana da cewa Hidimar zaben shugaban gidan majalisar dattijai na tara ne ke kawo jinkiri ga tsige ciyaman tarayyar Jam’iyyar APC ta Najeriya, kamrad Adams Oshiomhole.

Naija News Hausa ta fahimta cewa Jam’iyyar APC na son ne su zama da hadin kai don cin nasara da Jam’iyyar Adawa (PDP) a zaben Majalisar kamin su dauki mataki akan Oshiomhole.

4. Sojojin Najeriya sun kame ‘yan hari 5 a Jihar Katsina

Rundunar Sojojin Najeriya da ke a Jihar Katsina sun gabatar da kame masu sace-sacen mutane biyar a shiyar kauyan Sheme, a hanyar dajin Ruwan-Godiya da ke a Jihar.

Sojojin sun ci nasara da hakan ne a wata zagayen bincike na rukunin Sojojin ta Harbin Kunama 111.

5. Dalilin da ya sa ba za a bar binciken Saraki ba – Shugabancin Kasa

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta bada goyon bayan Hukumar Yaki da Cin Hanci da kuma kare Tattalin Arzikin Najeriya (EFCC), akan kadamar da bincike zargi ga shugaban sanatocin Najeriya, Bukola Saraki.

An bayyana hakan ne bisa bayanin Babban Ofisan Shari’a na Tarayya, Abubakar Malami, a yayin da yake mayar da martani ga zancen Saraki na neman a dakatar da bincike da ake yi akan sa.

6. Ooni na Ife zai jagoranci hidimar gargajiya a kasar Chicago

Sarkin Ife, da aka sani da suna Ooni of Ife, Oba Adeyeye Ogunwusi, yana a shirye don jagoran hidimar gargajiya na yaran Yarbawa da ke a Chicago, hadaddiyar kasar Amurka (USA).

Naija News Hausa ta samun tabbacin cewa za a fara hidimar ne a watan Satumba na shekarar 2019.

7. Dogara yayi bayani da zancen cewa yana son takara a Majalisar Dattijai ta Tara

Kakayin yada yawun Gidan Majalisar Wakilai, Hon. Yakubu Dogara, yayi watsi da jita-jitan cewa yana da muradin tseren takaran kujerar kakakin yada yawun Gidan Majalisar Dattijai na 9.

An bayyaya hakan ne a wata sanarwa da Turaki Hassan, mataimakin Dogara ga sadarwa ya bayar, da cewa ya zan dole ya bada haske ga wannan zancen karya da ya mamaye layin yanar gizo na cewa Dogara na neman fita takara a gidan Majalisar Dattijai.

Ka samu kari da cikakken Labaran Najeriya a shafin Hausa.NaijaNews.Com