Connect with us

Uncategorized

Sarkin Kano, Sanusi, ya bada Miliyan Biyar (N5m) don karban yancin ga wasu ‘yan gidan Yari

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00
Muhammadu Sanusi II

Mai Martaba Sarkin Kano, Malam Muhammad Sanusi II, a ranar Lahadi, 2 ga watan Yuni da ta gabata, ya bayar da kudi naira Miliyan Biyar (N5m) don karban yancin wasu ‘yan gidan jaru da ke a gidan yarin Kurmawa da ta Goron, a nan birnin Kano.

Naija News Hausa ta ruwaito a baya cewa Kotun Majistire ta Jihar Kano ta bada Umarni kame Mutane Ukku hade da Sanusi

A bayanin sarki Sanusi a lokacin da yake gabatarwa ga ‘yan gidan yarin da yake wa neman yanci, ya ce “Ina son ku gane da kuma daukar zama da rayuwar ku a gidan yari a matsayin nufin Allah, ina kuma gargadin ku da yin tunani mai zurfin don farfado da rayuwa mai kyau a yanzu da kuke batun samun yanci” inji mai Martaba.

Haka kazalika ya shawarce su da yin amfani da ‘yan sa’o’i kadan da ya saura a watan Ramadan don neman fuskar Allah ga rokon yafewar sa da kuma taimaka wa rayuwansu.

Ya gargade su da zama da rayuwar da ya dace, da cewa su guje wa halayen da zai iya mayar da su a gidan jaru.

Kwamturola Janar na Gidan Jarun Jihar Kano, Aliyu Yahuza, ya bayyana ziyarar Sarkin a matsayin abu mai muhinmancin kwarai da gaske. In ji shi “Wannan ya bayyana irin shugaba da Sarki Sanusi ya ke na nuna kulawa ga mutanen da yake jagoranci.”

KARATAN WANNAN KUMA; Jerin Sunaye da Lambobin da Sarkin Musulumai yace a Kira idan an gana da Fitar Watan Shawwal