Connect with us

Labaran Najeriya

Karya ne, Buhari bai Amince da kafa ‘Yan Sandan Jiha ba – Garba Shehu

Published

on

at

Listen to article
00:00 / 00:00

Shugaba Muhammadu Buhari ya gabatar da yin watsi da jita-jitan da ya mamaye layin yanar gizo da gidan labarai da zance cewa ya rattaba hannu da amince da sabon shirin kafa Hukumar ‘Yan Sandan Jiha da Kananan hukumomi a kasar Najeriya.

A wata sanarwa a Naija News ta shafin turanci, da kuma rahotannan gidan labarai, an sanar da cewa shugaba Muhammadu Buhari ya gabatar da rattaba hannu da kuma amince da kafa hukumar ‘yan sandan jiha.

Bisa bayanin kakakin yada yawun shugaba Buhari, Garba Shehu ya karyace zance, ya ce “Ba gaskiya bane cewa Buhari ya riga ya amince da dokar kafa ‘yan sandan Jiha, sai har an gabatar da farar takarda da ke dauke da amincewar shugaban kamin a iya sanar da bada tabbacin goyon bayan Buhari game da zancen” inji Garba.

“Lallai an gabatar da zancen a gaban shugaba Buhari, amma shugaban ya bukaci ayi binbini da bincike kwarai da gaske, a kuma mikar da farar takardan dokan nan da wata uku ta gaba kamin a dauki mataki ta musanman” inji shi.

KARANTA WANNAN KUMA; An Jefa wani Mutumi mai suna Hassan Garba a Kurkuku da laifin yin jima’i da yaro namiji mai shekaru 10