Connect with us

Uncategorized

2019: Ko da APC ta hana, sai na fita takaran kujerar mataimakin shugaban Sanatoci – Kalu

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Tsohon Gwamnan Jihar Abia, Mista Orji Kalu, ya gabatar da cewa zai fita tseren takaran kujerar mataimakin shugaban Sanatocin Najeriya ko ta yaya.

“Kowace mataki Jam’iyyar APC suka dauka, ba zai hana ni fita takaran neman kujerar mataimakin shugaban Majalisar Dattijai ba” inji Kalu.

Kalu a cikin bayanin sa ya gabatar da cewa zai fita takarar ne don tabbatar da cewa ya wakilci yankin Kudu maso gabashin kasar Najeriya.

“Bari in gaya maku gaskiya, ko da Jam’iyyar APC ta bukaci kada in fita takara, zan kauracewa hakan. Wannan matakin nada muhimanci a gareni da yankin mu, kwarai da gaske, ba zani yarda a barmu a baya ba ko kadan” inji Kalu.

Mista Kalu ya fadi wadannan kalamai ne a lokacin da yake wata gabatarwa a gidan talabijin Channels Television, inda ya bayyana cewa Gidan Majalisa ta 9 zata fi tsari da cika aiki mai kyau bisa majalisa ta 8 da suka sauka.

“Majalisa ta 9 zata kyautata wa al’ummar Najeriya duka”

“Muna cikin kadamar da shiri don gudanar da ayuka da suka dace a kasar, kuma za a bada dama a cikin tsare-tsare ga yankin kudu maso gabashin kasar. Ina kira da a ba gabashin kasar kujerar mataimakin shugaban gidan Majalisar Dattijai”

Mun ruwaito a baya a Naija News Hausa cewa daya daga cikin ‘yan shirin fina-finai a Kannywood, Kwararre da Fitacce, Jarumi Ali Nuhu ya rattaba baki ga zancen hidimar takaran zabe a kasar Najeriya.

Ali Nuhu, a ganawar shi da manema labaran BBC, ya ce “Muma muna da kudurin Fita takara a zaben Najeriya nan gaba”