Connect with us

Labaran Najeriya

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Alhamis, 6 ga Watan Yuni, Shekara ta 2019

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00
Manyan Labaran Jaridun Najeriya a Yau

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Alhamis, 6 ga Watan Yuni, 2019

1. Shugaban Kasar Ghana ya ziyarci Buhari

A ranar Laraba 5 ga watan Yuni 2019 da ta wuce, shugaban kasar Ghana, Nana Akufo-Addo ya kawo wa shugaba Muhammadu Buhari ziyarar kai tsaye.

A ganewar Naija News Hausa, Akufo-Addo ya ziyarci fadar shugaban Najeriya ne da tsakar ranar Laraba, a birnin Tarayya.

2. Hukumar NSCDC ta kame wani mai bayar da kayan hadin Bam ga Boko Haram

Hukumar tsaron Civil Defence ta Najeriya, NSCDC sun sanar da kame wani mutumi mai suna Aliyu Muhammed, da laifin samar da kayan hadain bama-bamai ga ‘yan ta’addan Boko Haram a Maiduguri, Jihar Borno.

Naija News ta gane da rahoton ne bisa sanarwar da kwamandan hukumar, Ibrahim Abdullahi ya bayar a ranar Laraba.

3. Ka manta da zancen Okorocha, bayyana shirin ka ga Jihar Imo – Nwosu na gayawa Gwamna Ihedioha

Dan takaran kujerar Gwamnan Jihar Imo ga zaben 2019 da aka kamala daga Jam’iyyar AA, Mista Uche Nwosu, ya gargadi Gwamnan Imo, Emeka Ihedioha da bayyana shirin da yake da ita ga al’ummar Jihar Imo, ya kuma manta da baiwa shugabancin tsohon Gwamnan laifi.

Nwosu ya fadi hakan ne don ganin cewa tun da aka rantsar da Ihedioha a matsayin gwamnan Jihar, sai surutu kawai yake da cewa ya cinma Jihar cikin mawuyacin hali da zai zan da matsala a gareshi.

4. Gidan Majalisar Wakilai zata kadamar da Hidimar Bankwana a ranar Alhamis

A yau Alhamis, 6 ga watan Yuni 2019, Gidan Majalisar Wakilai zasu gudanar da hidimar bankwana, a yayin da lokacin su a Ofishi ya kai ga karewa.

An bayyana hakan ne a wata sanarwa da aka bayar a birnin Abuja, daga bakin Mista Patrick Giwa, magatakardan majalisar.

5. Buhari zai ci nasara da matsalar tsaron kasar Najeriya – inji IBB

Tsohon shugaban kasar Najeriya a mulkin Sojoji, Ibrahim Badamasi Babangida, ya bayyana da bugun gaba cewa shugaba Muhammadu Buhari ya cika ga alkawalin sa na magance matsalar tsaro da kasar Najeriya ke fuskanta.

Ko da shike, Janar Babangida, ya kara da cewa kamin Buhari ya ci nasara da hakan, dole ne sai ya cika da daukan matakai na musanman.

6. Yadda shugaba Buhari ya lashe tseren zaben shekarar 2019  – APC

Jam’iyyar shugabancin kasar Najeriya, APC sun dage da cewa shugaba Muhammadu Buhari ya kayar da Alhaji Atiku Abubakar ne a zaben 2019 ba tare da wata magugi ko makirci ba.

Jam’iyyar sun fadi hakan ne a wata sanarwa da aka bayar a bakin magatakardan Jam’iyyar wajen sadarwa, Mallam Lanre Issa-Onilu, a ranar Laraba da ta wuce.

7. APC tayi kira ga Buhari da kafa baki ga zancen Oyegun da Oshiomhole

Mista Yekini Nabena, jigo a Jam’iyyar APC yayi kira ga shugaba Muhammadu Buhari da kafa baki zancen ganin laifi da ke tsakanin tsohon Ciyaman na Jam’iyyar APC, John Odigie-Oyegun da Ciyaman da ya maye gurbin sa, Adams Oshiomhole.

Yekini yayi wannan kirar ne a ranar Laraba, 5 ga watan Yuni don kula da matsalar bakar magana da kalubalanta da ke aukuwa tsakanin Odigie-Oyegun da Oshiomhole.

8. Bankin Tarayyar Duniya zata yada haske a yadda Abacha ya sace kudin Najeriya a baya

Bankin Tarayyar Duniya a ranar Laraba da ta wuce ta fada da cewa zata gabatar da haske a kan yadda tsohon shugaban Najeriya, Janar Sani Abacha, raunana asusun kasar a baya.

Naija News ta fahimta cewa Bankin sun bukaci a basu karin lokaci don su bayyana hakan.

10. JAMB ta ce bata sanar da kankanin Jimilar Makin 2019 da ake bukata a Jami’o’i ba

Hukumar Gudanar da Hidimar Jarabawan shiga Makarantar Jami’a babba, JAMB ta gabatar da cewa bata sanar da tukunna da jimilar maki da ake bukata ga shiga makarantu bisa jarabawa ta shekarar 2019 da aka yi a baya.

Hukumar ta bayyana hakan ne daga bakin jagoran sadarwa a layin yanar gizo, Dakta Fabian Benjamin, a birnin Legas da manema labaran NAN.

Ka samu kari da cikaken Labaran Najeriya a shafin Hausa.NaijaNews.Com