Connect with us

Labaran Najeriya

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Jumm’a, 7 ga Watan Yuni, Shekara ta 2019

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00
Manyan Labaran Jaridun Najeriya a Yau

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Jumm’a, 7 ga Watan Yuni, 2019

1. Abin Al’ajabi! an gano da Bu’tocin Alwalla fiye da dari a tsakar wata Icce

Wani sananne da Shahararran dan hadin fim a Najeriya mai suna Ernest Obi ya rabar da wata bidiyo a layin yanar
gizon nishadi da barin kowa da baki bude.

Naija News ta gane da cewa bidiyon na dauke ne da wata abin mamaki, a cikin bidiyon, an nino yadda butocin Alwalla fiye da dari ke fadowa a yayin da ake sarar wata Icce.

2. Dalilin da yasa Gwamnatin Jihar Zamfara ta dakatar da Sarakai biyu a ranar guda

Gwamnatin Jihar Zamfara ta dakatar da Sarkin Maru, Alhaji Abubakar CIKA Ibrahim da wakilin kauyan Kanoma, Alhaji Ahmed Lawal da zargin hada hannun da ‘yan ta’adda a Jihar.

Gwamnatin Jihar ta tsige ‘yan sarauta biyun ne bayan zarge-zarge da alamar da aka gane da su na hada kai da ‘yan hari don aiwatar da mumunar hali a yankin.

A haka kuma aka bukacesu da barin kujerar wakilcin su da kumar mikar da gurbin ga wasu har sai an gama bincike kan zargin.

3. Gwamnonin PDP da a shirye don biyar kankanin albashin ma’aikata ta N30,000 – inji Dickson

Gwamnonin Jam’iyyar Dimokradiyya, PDP sun gabatar da shirin su akan biyan kankanin albashin ma’aikata na naira dubu talatin (N30,000) da aka bada aminta da ita a baya a jagorancin shugaba Muhammadu Buhari.

Ciyaman na kungiyar Gwamnonin PDP, Mista Seriake Dickson , watau gwamnan Jihar Bayelsa ne ya bayanna hakan a wata ganawa da yayi da manema labarai, ranar Jumma’a, 7 ga watan Yuni 2019, a nan birnin tarayyar kasa, Abuja.

4. Dalilin da yasa na janye daga tseren takaran shugaban Gidan Majalisar Dattijai – Sanata Goje

Babban dan takaran kujerar shugabancin Gidan Majalisar Dattijai, Sanata Danjuma Goje, ya bayyana dalilin da yasa ya janye daga tseren neman zaben zama shugaban sanatoci a Najeriya bayan ganawa da shugaba Muhammadu Buhari.

Naija News Hausa ta gane da cewa Goje ya gana da shugaba Muhammadu Buhari tare da jagoran majalisar dattijai, Ahmad Lawan, da kuma wasu manya daga jam’iyyar APC, a fadar shugaban kasa, ranar Alhamis da ta gabata.

5. Gwamnonin Jihohin Najeriya 36 zasu gana da shugaba Buhari a yau

A yau jumma’a, 7 ga watan Yuni, shugaba Muhammadu Buhari yayi kirar ganawa da gwamnoni 36 da ke wakilcin jihohin Najeriya duka.

Naija News Hausa ta samu tabbacin hakan ne bisa wata sanarwa da aka bayar a hannun gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa a ranar Alhamis da ta gabata a birnin Asaba.

6. PDP ta kalubalanci Hukumar NBC da zancen dakatar da AIT

Jam’iyyar Dimokradiyya (PDP) ta bayyana rashin amincewa da matakin da hukumar Sadarwa ta Najeriya (NBC) ta dauka na dakatar da gidan talabijin na Daar Communications Limited, da ke hade da gidan Talabijin AIT

Naija News Hausa na da fahimtar cewa kamfanin Daar Communications Limited ita ce kamfanin da ke jagorancin gidan Talabijin AIT da Ray Power.

Ka samu kari da cikakken Labaran Najeriya a shafin Hausa.NaijaNews.Com