Connect with us

Labaran Najeriya

Miyetti Allah: Ba zamu bada Filin kiwo ga Fulani ba don Jihar mu – inji Ohanaeze

Published

on

at

Listen to article
00:00 / 00:00

Kungiyar zamantakewa da ci gaban Al’umma Iyamirai da aka fi sani da Ohanaeze Ndigbo, sun dage da cewa basu da wata fili da zasu bayar ga makiyaya Fulani don kiwo a Kudu maso gabas.

Kungiyar sun yi barazanar cewa ba zasu tsorata ba da barazanar mambobin kungiyar Miyetti Allah Cattle Breeders Association na cewar su bayar da fili ga makiyaya don kiwo a Kudu maso gabashin kasar Najeriya.

Naija News Hausa ta fahimta da cewa Ohanaeze sun bayyana hakan ne a wata taron Shugabannan kungiyar su da suka yi a ranar Alhamis, 6 ga watan Yuni da ta gabata a Enugu.

A hakan ne Nwodo yayi kira ga dukan Ndigbo da su zama da kula da kuma tsaro, musanman tabbatar da katange duk wata likin ta’addanci a yankunan su.

A bayanin Nwodo, ya fada da cewa “Ku jira umarni daga ‘yan uwanmu da ke a cikin siyasa, shugabannan Addinai da masu ruwa da tsaki, kungiyoyi a masana’anta duka.”

“Akan harkokin makiyaya a yankunan mu, motsi da tafiyar da ayuka ya zan da matsala ga mutanen mu”

“Abin takaici, duk da kokarin hukumomi tsaro don shan karfin su da dakatar da hare-hare, kadan kawai a cikin su aka iya kamewa ko kwace makamai da suke amfani da ita” inji Nwodo.

Nwodo ya kara da cewa don irin tashen karfin harin makiyaya, harma sun kai ga iya kame wakilin garin Daura, watau a garin shugaban kasar Najeriya har ga tsawon kwanaki 32.

Ka tuna mun ruwaito a Naija News Hausa a baya cewa ‘Yan Hari da Bindiga sun sace Surukin ma’aikaci ga shugaba Muhammadu Buhari a garin Daura, Katsina.