Connect with us

Uncategorized

Kalli dalilin da yasa wani rataya wa kansa igiya har ga mutuwa

Published

on

at

Naija News Hausa ta kula da cewa yanayin yadda mutane ke kashe kansu a kasar Najeriya na karuwa kullum, musanman mazaje.

Da safiyar yau, gidan labaran mu ta ci karo da bidiyon wani matashi kuma da ya rataya kansa da igiya har ga mutuwa.

Bisa bayanin da aka bayar ga manema labarai, mutumin ya rataya kanshi ne har ga mutuwa akan cewa yarinyar da suka yi soyayya da tsawon shekaru bakwai (7) ta yi watsi da shi da bin wani saurayi.

A cikin bidiyon, kaga yadda mutanen da suka shiga gidar sa ke kokarin fitar da igiyar a wuyan sa bayan ya riga ya mutu.

Zaka ji a cikin bidiyon yadda mutanen da ke kwance igiyar ke kuka da fadin “Shin ba kowa a gidar ne? Kalli yadda ka kashe kanka akan macce”

A yayin da ake kwance igiya a wuyar mutumin, zaka ji mutanen na fadin cewa “Shin babu kowa a gida ne? A haka kawai ka kashe kanka don Macce?”

Kalli Bidiyo a kasa kamar yadda aka bayar da ita;