Connect with us

Uncategorized

Yau kaine, gobe ba kai ba, Sanata Shehu Sani ya gayawa Ganduje game da zancen Sarkin Kano

Published

on

Sanatan da ke wakilcin Santira ta Jihar Kaduna a gidan Majalisar Dattijai, Sanata Shehu Sani, ya gargadi gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Ganduje, da janye daga zargi da kalubalantar da yake yi ga sarkin Kano, Muhammad Sanusi II.

Sanata Sani a wata sako da ya aika a layin yanar gizon Twitter, ya tunar da gwamnan da cewa “Ka tuna ita mulki da jagorancin abu ne na lokaci, yau kai ne, gobe kuma ba kai bane, duk abin banza ne” inji shi.

Kamar yadda muka sanar a labarai a baya da cewa Kotun Majistare ta Jihar Kano ta bada umarnin kame mutane biyu, hade da Sanusi.

Haka kazalika gwamnatin Jihar, a ranar Alhamis, 6 ga watan Yuni da ta gabata, ta bada takardar kalubalanta da bukatar sarki Sanusi ya bayyana cikin sa’o’i 24.

Naija News ta fahimta da cewa ana kalubalantar Muhammad Sanusi ne da laifin hada kai da kadamar da cin hanci da rashawa, da kuma sace kudi mai yawan gaske.

KARANTA WANNAN KUMA; An gano da Butocin Alwalla fiye da dari a tsakar wata Icce