Connect with us

Labaran Najeriya

Gwamnatin Tarayya ta gabatar da ranar 12 ga watan Yuni don Hutun ranar Dimokradiyya

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Naija News Hausa ta sanar a baya cewa Majalisar Dattijai da hadin kan Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta gabatar da ranar 12 ga watan Yuni a matsayin sabon ranar gudanar da hidimar dimokradiyya a kasar.

A yau Litini, 10 ga watan Yuni 2019, Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta sanar da hutu ga ‘yan makaranta da ma’aikata a ranar Laraba, 12 ga watan Yuni 2019, a matsayin ranar farko da za a girmama da kuma gudanar da sabon ranar Dimokradiyyar kasar Najeriya bisa ga yadda aka amince da sanar a baya.

An sanar da hakan ne a wata sanarwa da sakatare a Hukumar harkokin kasa, Baritsa Georgina Ekeoma Ehuriah ya bayar a wakilcin gwamnatin tarayya, inda kare hirar da taya ‘yan Najeriya da ke a gida da waje murna ga sabon ci gabar.

Bisa bayanin da aka bayar ranar Litinin daga bakin Daraktan sadarwa, Mohammed Manga ya bayar, yayi kira ga al’umar kasar Najeriya da girmama sadaukarwa da tsohin shugabannan kasar suka yi akan dimokradiyya, musanman wadanda suka rasa rayukan su a garin yin hakan.

An kare hirar da yin kira ga ‘yan Najeriya duka, hade da gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari da hada kai tare da juna don cinma guri kasar, musanman don jawo zamantakewar kwarai, zaman lafiya, ci gaba wajen karfafa tattalin arzikin kasar a hanyar da ya dace.