Uncategorized
Ku bamu Takardan Yancin Jagorancin Mu, Sanata a PDP na Jihar Bauchi da Mamba 4 sun kalubalanci INEC
Dan takaran kujerar Sanata a Jihar Bauchi a karkashin Jam’iyyar PDP, Alhaji Garba Dahiru, tare da wasu ‘yan gidan Majalisar Wakilai hudu da Kotun Koli ta bayar da umarni ga Hukumar INEC da basu takardan komawa kan mulki, sun kalubalanci INEC da su bi umarnin Kotu don bayar da takardan a garesu.
Naija News ta gane da zancen ne bisa gabatarwa da aka bayar ga manema labarai a wata taro da ya kumshi ‘yan takara daga Jam’iyyar PRP, NNPP da PDP, inda Dahiru ya bayyana da cewa duk da cewa Kotun Kara ta bada da dama da umarni ga Hukumar INEC da bayar da takardan yancin, INEC ta ki bin hakan.
Ka tuna da cewa a ranar 16 ga watan Mayu 2019 da ta gabata, Kotun neman yanci, a jagorancin Alkali Bello Kawu a falen kara mai lamba FCT /HC/CV/988/2019, ya bada umarni ga Hukumar gudanar da zaben kasar Najeriya (INEC) da mikar da takardan yancin jagoranci ga dan takara da ya zan na biyu ga tseren zaben kujerar Sanatan Kudu ta Jihar Bauchi, hade da ‘yan majalisar wakilai hudu da ke a yankunan Jihar.
‘Yan Gidan Majalisar Wakilai hudu sune kamar haka; Abdulkadir Ibrahim, Alkaleri/Kirfi (PDP), Dayyabu Chiroma, Darazo/Ganjuwa (PRP), Awwal Jatau, Zaki (PDP) da kuma Isa Mohammed Wabu.
KARANTA WANNAN KUMA; Matan Tsohon Gwamnan Jihar Taraba, Hausa Suntai ta sake Aure da wani dan Matashi mai shekaru 30.