Connect with us

Labaran Najeriya

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Litinin, 10 ga Watan Yuni, Shekara ta 2019

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

 Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Litinin, 10 ga Watan Yuni, 2019

1. Tsohon Ministan Shugaba Buhari zai fuskanci Hukunci

Tsohon shugaban Shari’an Tarayya da kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami, zai fuskanci ganawa da hukunci a ranar Jumma, 14 ga watan Yuni ta gaba.

Naija News Hausa ta fahimta cewa hakan zai faru ne da Malami bisa wata furci da yayi ga tsohon Jami’in bada shawara ga shugaban kasa a lamarin tsaro, Sambo Dasuki.

2. PDP na zancen kalubalantar shari’ar Kotu akan bayar da takardan yanci ga Okorocha

Mista Jones Onyeriri, dan takaran kujerar Sanata a karkashin Jam’iyyar PDP ta Jihar Imo, ya rantse da kalubalantar shari’ar da kotun tarayya tayi na bada umarni ga Hukumar INEC don bayar da takardan yancin kujerar Sanata ga Rochas Okorocha.

A wata gabatarwa da aka yi ga manema labarai a ranar Asabar da ta wuce, Darakta Janar na neman takara ga Jones Onyeriri, Mista Eze Ugochukwu ya kalubalanci Alkali Okon Abang, na kotun kolin tarayya da yin makirci.

3. Ba Oyegun ne ke bayan bakin jinin Oshiomhole ba – inji Erhahon

Tsohon kakin yada yawun Jam’iyyar APC ga lamarin zabe, Comrade Erhahon, ya bayyana da cewa ba tsohon ciyaman na Jam’iyyar, John Odigie-Oyegun ne ke da sanadiyar matsalar da Adams Oshiomhole ke fuskanta ba.

“Zargin Oyegun zai sa ne kawai matsala ta karu, amma ba shi ne sanadiyar rashin farin jinin Oshiomhole ba” inji shi.

4. Rashin sakin jerin Ministoci da Buhari yayi ya tada cece-kuce

Matakin da shugaba Muhammadu Buhari ya dauka na kin gabatar da jerin sunayan sabbin Ministoci da zasu yi jagoranci a mulkin sa ta karo biyu, ya bar manyan ‘yan siyasa da cece kuce, a yayin kowa ko hange da jira.

A ganewar Naija News shugaba Buhari ba zai iya gabatar da jerin Ministocin ba a yayin da ba a kamala hidimar zaben shugaban da zai jagoranci Majalisar Dattijai na 9 ba.

5. Akpabio ya bayyana wanda ke da sanadiyar faduwar sa ga tseren Sanata

Tsohon Gwamnan Jihar Akwa Ibom, Mista Godswill Akpabio na zargin jami’in hukumar INEC da ya jagoranci zaben Jihar Akwa Ibom, Mike Igini da zama sanadiyar faduwar shi ga zaben Jihar.

Akpabio ya fadi hakan ne a wata gabatarwa da yayi a karamar hukumar Essien Udim ta Jihar, a yayin da yake bada wata bayani ta musanman ga mambobin yankin sa.

6. Bana bukatar Buhari ko wasu a kasar kamin in zam shugaban gidan Majalisa – inji Ndume

Sanatan da ke wakilci a karkashin Jam’iyyar APC ta Jihar Borno, Ali Ndume ya ce goyon bayan shugaba Muhammadu Buhari ko wasu ‘yan gidan majalisar bai zama da muhinmanci ba ga neman zaben sa a kujerar shugabancin gidan Majalisa.

Naija News da na fahimtar cewa fiye da ‘yan gidan majalisa 60 suka riga da bada goyon baya ga Sanata Ahmed Lawan, Sanata a jam’iyyar APC daga Arewacin Yobe, da zama shugaban gidan Majalisar Dattijai.

7. Hukumar ICPC na kan bincike ga dan Majalisar Wakilai a Jam’iyyar PDP

Dan Majalisar wakilai a karkashin Jam’iyyar PDP, da ke wakilci a Jihar Delta, Mutu Ebomo na karkashin binciken hukumar binciken Cin Hanci da Rashawa da Laifuka (ICPC) akan wasu zargi.

An bayyana da cewa Mista Mutu Ebomo ya bayar ne da takardan sakandiri mara sa kyau da kuma takardan babban makarantan Jami’a wanda bashi da kyau kuma a hidimar zabanni da aka yi a baya.

Ka samu cikakke da karin Labaran Najeriya a shafin Hausa.NaijaNews.Com