Uncategorized
Sabuwar Hadarin Mota ya dauke Rayuka Shidda a Jihar Sokoto
Wata hadarin Mota da ta faru a ranar Lahadi, 9 ga watan Yuni da ta gabata, a Jihar Sakwato ya tafi da rayuka Shidda.
Bisa rahoton da Hukumar kula da harkokin hanya (FRSC) suka bayar ga Naija News, akwai tabbaci da mutuwar mutane 6, a yayin da kimanin mutane 15 kuma suka samu raunuka.
Kwamandan Hukumar FRSC ta Jihar, Mista Muhammad Kaugama-Kabo, a yayin da yake bada bayani ga kungiyar manema labaran Najeriya (NAN), ya bayyana da cewa hadarin ta faru ne da wata doguwar mota mai lamba JEG 664 XA.
Ya kara da cewa hadarin ya faru ne a yayin da motar ke kan tafiya, dauke da mutane da kayaki cikke a ciki. “Da isar motar a babban hanyan Sokoto zuwa Birnin Kebbi, a nan hadewar hanya da ke kusa da Gidan Man Ada, sai kawai motar ta kihe da mutane da kayaki da ke a cikin ta” inji shi.
“Motar ita kade ta yi hadari, kuma laifin direbar motan ne, sanadiyar mugun gudu da yake yi” inji Mista Muhammad.
“Motar na dawowa ne da kaya da mutanen da ke a ciki daga garin Ibadan zuwa Illela, karamar hukuma a Jihar Sokoto”
Mista Muhammad ya ci gaba da bayyana cewa anan take mazaje shidda suka mutu, mutane 15 kuma dauke da mugan raunuka.
“A halin yanzu mutanen da suka sami rauni na a Asibitin Usman Danfodio, inda ake basu kulawa ta gaske” inji shi.
Shugaban FRSC, a hakan ya gargadi matafiya kan hanya da janyewa daga mugun gudu da sukan yi idan suna kan tafiya.
Ya kuma karshe da kira ga mutane don zuwa Asibitin da ke a UDUTH don bincike da gane ko watakila akwai ‘yan uwan su a cikin hadarin.
KARANTA WANNAN KUMA; ‘Yan Makarantan Jami’ar Kwaleji Fiye da 6, a Jihar Sokoto sun Mutu a wata Hadarin Mota