Connect with us

Uncategorized

Gobarar Wuta ya kame shaguna Shidda a Kasuwar ‘Yan Rodi a Jihar Kano

Published

on

at

Shaguna Shidda sun kame da gobarar wuta a Jihar Kano ranar Lahadi da ta gabata

Wasu sabbin shaguna shidda a ranar Lahadi da ta wuce a shiyar kasuwar Kofar Ruwa (Kasuwar ‘Yan Rodi) da ke a Jihar Kano, ya kame da gobarar wuta.

Kakakin yada yawun hukumar yaki da gobarar wuta na Jihar Kano, Malam Saidu Mohammed, a birnin Kano ranar Litini da ta wuce ya bada tabbacin gobarar wutar ga manema labarai, ko da shike ya fada da cewa harwa yau basu iya gane da sanadiyar gobarar wutan ba tukunna.

A cikin bayanin Mista Saidu, ya bayyana da cewa hukumar su ta karbi kirar gaugawa ne daga wani mutumi mai suna Usman Danladi, a missalin karfe goma na daren ranar Lahadi da cewa gobara ya kame da kasuwar.

”Da zarar da muka karbi kirar, hukumar ta aika a gaggauce da ma’aikata don dakatar da yaduwar wutar, sun kuma sami isa ga wajen a missalin karfe 10:15 na dare don dakatar da yaduwar wuta ga sauran shagunan” inji shi.

Ko da shike ya bada haske da cewa ba wanda yayi rauni ga gobarar wutan, amma dai an yi rashin kayaki da dama.

Mista Saidu ya gargadi masana’anta da zama da kula da kuma yin hankali da duk wata abin da zai iya jawo gobara a cikin kasuwa nan gaba.

Ka tuna mun sanar a Naija News Hausa a baya cewa Wasu Mutane bakwai sun kuri Mutuwa a wata Gobarar Wutan Motar Tanki da ya faru a shiyar Jihar Benue.Advertisement
close button