Labaran Najeriya
Kalli bidiyon Lokacin da Shugaba Buhari ya isa ga Hidimar Dimokradiyya
Ranar Dimokradiyyar Najeriya – 12 ga watan Yuni 2019
Shugaba Muhammadu Buhari da matarsa Aisha Buhari sun isa filin wasan Eagles Square, wajen hidimar sabon ranar Dimokradiyyar Najeriya da aka canza zuwa ranar 12 ga watan Yuni.
Kamar yadda rahotannai suka bayar ga Naija News, shugaba Buhari da matarsa sun halarci filin wasan ne a missalin karfe goma da kwata (10:15) na safiyar yau Laraba, 12 ga Yuni.
Kalli bidiyon a kasa;
Mr. President @MBuhari arrives to Eagle Square for #DemocracyDay pic.twitter.com/0WWU7YzNhq
— White Nigerian (@whitenigerian) June 12, 2019
Ko da shike, kamin halartan shugaba Buhari, mataimakin sa, Farfesa Yemi Osinbajo, Shugabanan Hukumomin Tsaro, Babban Alkalin Najeriya (CJN), Shugaban Gidan Majalisar Dattijai da Wakilai hade da manyan ‘yan siyasan Najeriya da wakilai daga kasashen waje sun riga sun kama kujerar su, a yayin da ake jirar shugaba Muhammadu Buhari da isowa.
Ka tuna da cewa kasar Najeriya a da takan gudanar da hidimar Dimokradiyya ne a ranar 29 ga watan Mayu a kowace shekara, har sai da shugabancin Najeriya a jagorancin shugaba Buhari ta amince da canza ranar zuwa ranar 12 ga watan Yuni don tunawa da Jarumai da suka yi gwagwarmaya da sadaukarwa ga Najeriya don neman yancin Dimokradiyya a shekarun baya da suka shige. Musanman tsohon shugaban Najeriya, da aka fi sani da MKO Abiola.
KARANTA WANNAN KUMA; Wani Limami ya Mutu a yayin da yake bada Lakca a ranar Jumma’a da ta wuce.