Connect with us

Labaran Najeriya

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Laraba, 12 ga Watan Yuni, Shekara ta 2019

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Laraba, 12 ga Watan Yuni, 2019

1. Buhari Jarumi ne wajen yaki da Cin Hanci da Rashawa – Kagame

Shugaban kasar Rwanda, Paul Kagame ya bayyana shugaba Muhammadu Buhari da zaman Jarumi na musanman a yaki da Cin Hanci da Rashawa a kasar Afrika.

Kagame ya kara da yin kira ga dukan shugabannai a kasar Afrika da sadaukar da kansu ga yaki da cin hanci da rashawa.

2. JAMB ta saki tsarin lambar maki da ake bukata da shiga Jami’o’i a shekarar 2019

Hukumad gudanar da Jarabawan shiga babban Makarantan Jami’a (JAMB) a ranar Talata, 11 ga watan Yuni, ta sanar da lambar kankanin maki da ake bukata a makarantu don shiga karatu a Jami’a a shekarar 2019.

Naija News Hausa ta fahimta da cewa hukumar sun gabatar ne da hakan bayan da suka kamala wata taron hukumar.

3. Ahmed Lawan ya lashe zaben kujerar shugaban Sanatocin Najeriya na 9

Dan takaran kujerar shugaban Sanatocin Najeriya a Majalisar Dattijai na 9, a karkashin Jam’iyyar APC, Sanata Ahmed Lawan a ranar Talata da ta wuce ya ci nasara ga tseren zaben shugaban Gidan Majalisar Dattijai da aka yi tsakanin sa da Ali Ndume, dan takara daga Jam’iyyar PDP.

Naija News Hausa ta sanar da cewa Sanata Lawan ya lashe zaben ne da yawar kuri’u 79, fiye da na dan adawan sa.

4. Ovie Omo-Agege ya lashe kujerar mataimakin shugaban Gidan Majalisar Dattijai na 9

Dan takaran mataimakin shugaban Gidan Majalisar Dattijai na 9, daga Jam’iyyar APC, Sanata Ovie Omo-Agege ya ci nasara da tseren zaben kujerar.

Hakan ya faru ne bayan da Ovie Omo-Agege ya fiye dan adawan sa, Sanata Ike Ekweremadu da yawan kuri’u.

5. Dan shekara 34 ya ci zaben dan Majalisa a Jihar Kwara

Sabon ci gaba a Najeriya a yayin da wani dan shekara 34 ga haifuwa, Yakubu Saliu Danladi ya lashe kujerar zama dan Majalisa a Jihar Kwara.

Naija News Hausa ta gane da cewa Danladi ne mamban gidan Majalisa na farko a yankin Ilesha-Gwanara, a Jihar Kwara.

6. Femi Gbajabiamila ya ci zaben kakakin Majalisar Wakilai

Mista Femi Gbajabiamila ya ci nasara da lashe zaben Majalisar Wakilai na 9 a ranar Talata, 11 ga watan Yuni 2019.

Bisa ga hidimar zaben shugaban gidan Majalisar wakilai da aka gudanar a ranara Talata da ta wuce, Mista Femi ya lashe zaben da yawan kuri’u 283, wanda ya bayyana kada dan adawan sa, Umar Bago mai yawan kuri’u 76.

7. Wase ya lashe kujerar mataimakin kakakin gidan Majalisar Wakilai na 9

Mista Ahmed Idris Wase ya ci nasara a hidimar zaben mataimakin kakakin yada yawun Majalisar wakilai da yawar kuri’u.

Ka tuna a ranar jiya Talata, 11 ga watan Yuni aka gudanar da hidimar zaben shugabancin Gidan Majalisai biyu a kasar Najeriya.

8. A karshe Hukumar INEC ta bayar da takardan shiga Majalisa ga Okorocha

Hukumar Kadamar da Hidimar zaben kasar Najeriya, INEC ta baiwa tsohon gwamnan Jihar Imo, Rochas Okorocha takardan yancin zama sanata a Najeriya.

Hakan ya faru ne bayan wata ganawa da hukumar tayi a ranar Talata da ta wuce.

9. APC da shugaba Buhari na rokon Kotun Neman Yanci da dakatar da Kara

Jam’iyyar Shugabancin kasar Najeriya da shugaba Muhammadu Buhari na rokon Kotun Neman Yanci da ke jagorancin karar zaben watan Fabrairu da su janye karar da Atiku Abubakar ya gabatar.

Ka tuna da cewa karar ta kai ga kotu ne bayan da Atiku Abubakar da wasu ‘yan takaran shugaban kasa daga sauran Jam’iyu suka bayyana rashin amince da Muhammadu Buhari a matsayin mai nasara ga zaben 2019.

10. Najeriya na murna da ranar 12 ga watan Yuni a matsayin sabon ranar Dimokradiyya

A yau Laraba, 12 ga watan Yuni 2019, kamar yadda aka sanar a baya, kasar Najeriya na gudanar da hidimar murna da sabon ranar Dimokradiyya da aka amince da ita a baya a jagorancin shugaba Muhammadu Buhari.

Hakan ya kasance ne don tunawa da kuma girmama sadaukarwa da Jarumai suka yi na karban yanci Dimokradiyya ga kasar Najeriya a shekarun baya da suka shige.

Ka samu kari da cikakken Labaran Najeriya a shafin Hausa.NaijaNews.Com