Connect with us

Uncategorized

Rundunar Sojojin Najeriya sun ribato Matan Aure biyu da Yara Shidda a hannun Boko Haram

Published

on

Rundunar Sojojin Najeriya sun sanar da ribato Matan Aure biyu tare da yara kanana shidda daga hannun ‘yan ta’addan Boko Haram a shiyar kauyan Gwadala, a Jihar Borno.

Bisa rahoton da aka bayar ga Naija News, Sojojin sun ci nasara da hakan ne bayan wata yawon zagaye da suka kadamar a nan yankin Gwadala, Jihar Borno.

Naija News Hausa ta gane da cewa rundunar sojojin da ke a yankin sun ci nasara da kashe daya daga cikin ‘yan ta’addan Boko Haram a shiyar ba da dadewa ba.

Gidan labaran nan tamu ta karbi wannan rahoton ne bisa wata sanarwa da aka bayar daga mataimakin Daraktan Rundunar Sojojin, da kuma Ofisan samar da labarai ga sojojin, Col. Ado Isa, a ranar Laraba, 12 ga watan Yuni 2019.

Mun ruwaito a Naija News Hausa a baya da cewa an Kashe akalla mutane 18 a wata sabuwar harin ‘yan ta’adda a Jihar Sokoto.

An bayyana kuma da cewa Ciyaman din da sauran hukumomin tsaron Jihar sun ziyarci kauyan Rakumni, Tsage da kuma Kalgo don ceton rayuka da kuma ta’aziya, anan kazalika suka tattara gawakin mutanen da aka kashe don shirya su ga hidimar bizinewa.