Connect with us

Labaran Najeriya

Kalli Alkawarin da Shugaba Buhari yayi ga Matalauta Miliyan 100 a Najeriya

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Shugaba Buhari yayi sabon alkawari ga Matalauta Miliyan 100 a kasar Najeriya

A ranar Laraba da ta gabata, Shugaba Muhammadu Buhari, a yayin da yake gabatarwa wajen hidimar sabon ranar Dimokradiyyar kasar Najeriya, yayi sabon alkawari da cewa zai tabbatar da ganin cewa Matalauta akalla Miliyan 100 sun koma ga wadata a kasar Najeriya nan da shekaru goma.

Naija News Hausa ta gane da rahoton ne a bayanin Buhari a filin Eagles Square ta birnin Tarayya, watau a lokacin da yake gabatarwa ranar 12 ga watan Yuni, sabon ranar Dimokradiyyar Najeriya.

Shugaban ya fada da cewa shugabancin sa zata tabbatar da cewa ta karfafa tattalin arzikin kasar Najeriya da kuma tabbatar da ganin cewa Matalauta sun koma ga wadata.

“Asusun Kayan Tsarafawar mu (GDP) ya kamata ya karu da kashi 2.7% a karshen wannan shekara” inji shugaban

“Haka kuwa kayan jari da kasar ke da ita a waje ya karu da Dala 45 wanda ya isa ya biya bukatar da ake da ita nan da watannai tara”

“A farko dai zamu tabbatar da karfafa tattalin arzikin kananan hukumomi ta wurin samar da kayakin aikin gona ga manoma, da kuma tallafawa masu sana’a iri-iri, da kuma samar da hanyoyin da zai taimaka ga tafiyar da ayuka”

“Na biyu kuma, dukan masana’anta kanana da manya zasu samu rabon kayaki da zai karfafar da sana’arsu, don kara ga tattalin arzikin kasar da rayuwar al’umma gaba daya” inji Buhari.

A karshe, shugaban yace a cikin wannan shugabanci nasu ta karo biyu, zasu tabbatar da tafiyar da jagoranci yadda ya dace, musanman magance matsaloli da ya isa kulawa a kasar Najeriya duk a cikin shekaru 4 da ke gaba.

Ka tuna da cewa shugaba Muhammadu Buhari yayi barazanar cewa shugabanci sa zata kai Najeriya ga NEXT LEVEL a karo ta biyu.

Shugaban ya fadi hakan ne a wajen zaman liyafa da yayi a fadar sa daren ranar Talata da ta gabata.