Connect with us

Uncategorized

Tarihi, Al’adu Da Asalin Hausawa a Afrika

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00
Asalin Hausawa a Afrika

Shin daman baka san Tarihi da Asalin Mallam Bahaushe ba? Karanta a kasa!

Kamar yadda kowane yare ke da Asalin ta, haka kazalika Hausawa ke da tasu asali. Duk da cewa kusan babu inda zaka shiga a kasar Najeriya, hadi da wasu kasashen Afrika, kai, harma a Turai zaku iske mallam bahaushe, duk da hakan suna da Asali mai tasirin gaske.

Kabilar Hausa wata kabilace da ke zaune da kuma yawaita a arewa maso yammacin taraiyyar kasar Najerya da kuma kudu maso yammacin jamhuriyyar Nijar. Kabilar Hausa na da dimbin al’umma kwarai da gaske, amma kuma a al’adance mai matukar hadaka.

Bincike ta nuna da cewa; akalla akwai sama da mutane miliyan hamsin da harshen Hausa yake asali a gare su, duk da cewa a tarihance kabilar Hausawa na tattare a salasalar birane daban daban.

Ko da shike kamin aka rabar da Jihohi a kasar Najeriya, akwai sassa da aka sani tun asali a kasar da harshen Hausa. Sune kamar haka;

Daura, Kano, Katsina, Zaria, watau Zazzau, Gobir, Rano da Biram.

Waddanna sune garuruka da aka sani a tahirance da yaran Hausa a kasar Najeriya tun shekaru lu’u lu’u da suka gabata.

Shekarar da aka fidda Kabilar Hausa

Hausawa dai a tarihance sun sami kafa daularsu ne tun daga shekarar 1300’s da ya gabata. Hakan ya yiwu ne sa’adda suka sami nasarori da dauloli kamar su Daular Mali Songhai, Borno da kuma Fulani. A wanna lokutan, Hausawa sun cika da gagarimin ikon, mulki da hadaka ta kau da baki’yan neman ruwa da tsaki, da kuma neman angizon a cikinta da kuma harkallar bayi.

A farkon shekarar 1900’s, a sa’adda kabilar Hausa ke yunkurin kawar da mulkin angizo na fulani, sai turawan mulkin mallaka ta Birtaniya suka mamaye arewancin Najeriya, da kuma kafa manufofin mulkin bayan gida, a bisa karkashin mulkin Birtaniya, a hakan ‘yan mulkin mallaka sai suka marawa fulani baya na cigaba da manufofin angizon siyasarsu. Har yanzu dai mulkin kamin gambiza tsakanin Hausawa da Fulani shi ne yayi kane-kane a arewacin Najeriya. Hadakar gamin kambiza dai an kafa ta ne tun asali a matsayin fulani su dare madafun ikon a tsararren tsarin siyasar arewa. Akasarin masu mulki na fulani sun kasance yanzu, a al’adance hausawa gwamitse.

Ko da shike, Hausawa na farko maharba ne, amma da zuwan addinin Islama, bayan suka karba kuma da hannu biyu sai labari ya sha bambam.

Ginshikokin al’adun hausawa na da mutukar zaranta, kwarewa da sanaiya fiye da sauran al’ummar dake kewayenta.

Menene Sana’ar Mallam Bahaushe?

Tun a farko, Noma ita ce babbar sana’ar hausawa, harma hausawa kan yi ma sana’ar noma kirari da cewa, “na doke tsohon ciniki kowa yazo duniya kai yatarar.” Ko da yake akwai kuma wasu sana’o’i kamar su sha’anin Jima, watau harkar Fatu, Rini, Tsaka da Kira.

Hausawa dai sun jima da shahara wajen harkar fatauci, kana kuma masu arziki na taka rawa a sha’anin yau da kullum, tare da masu mulki da masana. Bincike da tarihi ya bayyana harshen Hausa da harshe mafi girma da kuma mafi sanai’yar harshe a nahiyar Afirka gaba daya. harshen hausa ya aro wasu kalmomi daga wasu harsuna musamman larabci, kana kuma harshen na tafiya tare da yanayin mu na zamani bisa al’adar cudeni- na cudeka.

Mun ruwaito a Naija News Hausa a baya da Ire-Iren abincin Mallam Bahaushe da kuma yadda ake shirya Kilishi