Connect with us

Uncategorized

Karshen Zamani! Wani yayi wa Uwarsa Fyaden Dole

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Karshen zamani ta iso a yayin da wani yayi wa Maman da ta haife shi fyade

Hukumar Tsaron Civil Defence Corps ta Jihar Imo sun gabatar da kame wani mutumi da ake kira Paul Ihuaku, da zargin kwanci da tsohuwar da ta haife shi.

Naija News Hausa, bisa rahotannai da aka bayar, an bayyana cewa dan shekaru 45 ga haifuwar, Paul mazauni ne na shiyar Umueke Ezagbogu, a nan karamar hukumar Ezinihitte Mbaise ta Jihar Imo.

A bayanin kwamandan hukumar Civil Defence ta Jihar Imo, Mista Raji Ibrahim, ya bayyana a ranar Alhamis da ta gabata da cewa hukumar su ci nasara da kame Paul ne bayan da suka karbi kira daga mazauna.

Bisa rahoto, maman Paul ne tayi karar sa ga matasan da ke a unguwar bayan da kadamar da halin kyamar da ita, sai kuma matasan suka yi sanar da hukumar tsaro ba tare da jinkiri ba.

“A bayan da hukumar mu ta karbi rahoton abin da Paul yayi sai aka aika da jami’an tsaro a wajen don kame shi nan take” inji Mista Raji.

Ko da shike an bayar da cewa Paul ya fada ga hukumar cewa lallai yayi hakan ne bisa buguwa da kayan maye.

“A maraicen ranar, na riga na bugu da giya, na wanke kaina tas da kayan maye, ba abin da nake ji ko muradi a lokacin sai yin jima’i. A hakan ne na tsorata tsohuwa na don kwanci da ita” inji Paul.

Da aka tambayi mutumin ko wata kila yana da Aure, sai yace a’a baya da mata saboda baya da aikin yi ko wata hanyar bida.

“Ba wai an yi mani Sihiri ko cinuwa ba, kayan maye ne kawai ya kaini ga hakan” inji shi.

“Ina cikin dakin sanwa ne a yayin da na hangi Paul da bindiga a hannun sa. Ya tsoratani da kuma barazanar kashe ne da bindigar idan na ki kwanci da shi. Ban iya yin komai ba, dole na roke shi da yin abin da ya bukace ni da yi” inji maman Paul.

“Dole ne nayi kira ga matasan unguwar da gari ya waye don abin ya faru ne da duhun dare, na kuma sanar da su da abin da ya faru. Jin hakan ne matasan suka sanar da Jami’an tsaron NSCDC da ke a yankin hedkwatan Itu” inji ta.

Mun ruwaito a Naija News Hausa a baya da cewa Jami’an tsaro sun kame wani Tsoho Mai Shekaru 72 da ke yiwa ‘yan makaranta fyade.

An yi nasara da kame tsohon ne bayan da wani mazaunin unguwar ya gane da jin motsi da kuma ji tsuwa na fita daga dakin tsohon, garin bincike da leken ko menene ke faruwa, sai ya gane da cewa tsohon ne ke yin jima’i da kananan yara.