Connect with us

Labaran Najeriya

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Jumma’a, 14 ga Watan Yuni, Shekara ta 2019

Published

on

at

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Jumma’a, 14 ga Watan Yuni, 2019

1. Abokin takaran Uche Nwosu ya koma ga Jam’iyyar PDP

Mista Iheanacho Ihim, abokin takaran Uche Nwosu ga neman kujerar gwamnan Jihar Imo daga Jam’iyyar Action Alliance (AA), ya koma ga Jam’iyyar Dimokradiyya (PDP).

Tsohon kakakin yada yawun ya koma ga Jam’iyyar PDP ne a ranar Alhamis da ta a lokacin da ake gabatarwa a gidan Majalisar Jihar.

2. Atiku Vs Buhari: Election Tribunal Takes Decision On Atiku’s Request To Access INEC Server

Jagorancin Kotun Neman yanci ta bada hadin kai ga bukatar dan takaran kujerar shugaban kasar Najeriya a zaben 2019 daga Jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, don binciken kayakin da aka yi amfani da su a wajen hidimar zaben watan Fabrairu.

Alkali Mohammed Garba da ya jagoranci karar a ranar Alhamis da ta wuce ne ya gabatar da hakan bayan karban bayanai daga masu kara.

3. Hukumar INEC ta mayar da martani ga zancen PDP da Atiku akan amfani da na’urar sadarwa a zabe

Hukumar Gudanar da hidimar Zaben kasar Najeriya (INEC) ta yi watsi da zancen Atikua Abubakar akan amfani da na’urar sadarwa don ajiye sakamakon zaben shugaban kasa ta ranar 23 ga watan Fabrairu 2019.

Naija News Hausa ta fahimta da hakan ne bisa bayanin da hukumar tayi a ranar Alhamis da ta wuce.

4. Buhari ya bada goyon baya ga kafa Jamhuriyar Sahrawi

A ranar Alhamis da ta gabata, shugaba Muhammadu Buhari ya nuna bada goyon baya ga Sahrawi Arab Democratic Republic (SADR) a bukatar su na neman yanci da dayantaka.

An bayyana hakan ne ga Naija News bisa sanarwan da mai bada shawarwari ga Buhari a lamarin sadar da labarai, Mista Femi Adesina ya bayar.

5. An sanay Abaribe matsayin shugaban karamar Majalisa

Sanatan da ke wakilci daga Jihar Abia a Jam’iyyar Dimokradiyya (PDP), Enyinnaya Abaribe ya lashe matsayin zaman shugaba ga karamar ‘yan Majalisar Dattijai na 9.

Naija News Hausa na da sanin cewa Abaribe ya ne da matsayin mataimakin gwamnan Jihar Imo, a bayan jagorancin Orji Uzor Kalu a shekarar 1999.

6. Wata Jam’iyyar Adawa ta gabatar da sabon bukata ga Kotun Neman Yanci

Daya daga cikin Jam’iyu da suka gabatar da karar rashin amincewa da nasarar shugaba Muhammadu Buhari a zaben 23 ga Fabrairu 2019, sun gabatar da sabon sharadi ga Kotu.

Jam’iyyar Hope Democratic Party (HDP) da dan takarar su a zaben 2019, Albert Oworu, sun bukaci kotu da janye karar shugaban kasa da ke a kotu.

7. An rantsar da Rochas Okorocha a Jihar Imo

Bayan da aka bayar da takardan yancin da wakilci a Majalisar Dattijai ga tsohon gwamnan Jihar Imo, Rochas Okorocha, an rantsar da shi kuma a matsayin Sanata a Najeriya.

An gudanar da hidimar rantsarwan ne a jagorancin magatakardan Majalisar, Sanata Nelson Ayewoh.

8. Majalisar Dattijai sun daga zama zuwa ranar 2 ga Yuli 2019

Gidan Majalisar Dattijai ba za su yi zama Majalsa ba har ga tsawon mako biyu, a yayin da aka daga zaman Majalisar zuwa ranar 2 ga watan Yuli 2019.

Naija News ta fahimta da cewa Majalisar ta bada hutun ne don su samu daman hada kai da kwamitin aikace-aikace wajen gabatar da matsayi ga Ofisoshi.

Ka samu kari da cikakken Labaran Najeriya Najeriya a shafin Hausa.NaijaNews.Com