Connect with us

Uncategorized

Barayi sun kashe ‘yan Kabu-Kabu biyu a Jihar Kaduna a Yau

Published

on

at

A yau Litini, 17 ga watan Yuni, Naija News Hausa ta karbi rahoton barayi biyu da suka tari ‘yan kabu-kabu biyu, suka kwace babur dinsu, suka kuma kashe su bayan da suka kwace wayoyin salula da suke da shi.

Abin ya faru ne a yau da safiyar Litini, bakin wata gidan man fetur na Usmania da ke a hanyar babban hanyar Nnamdi Azikwe nan Jihar Kaduna.

Daya daga cikin ‘yan kabu-kabu da barayin suka hara, Rayyanu Yahaya Dawakin Tofa, ya bayar ga manema labarai da cewa harda shima an kwace masa wayar salula da kudin da yake tare da shi.

“Muna kwance ne a nan cikin gidan Man Fetur na Usmania, sai kwaram suka fado mana da makamai kamar Yuka da Bindigogi suna barazana da su. Sun bukace ni da mika masu wayana da kudaden da ke a hannu na, ba tare da jinkiri ba sai na bi umarnin su na mika masu, daya daga cikin su kuma ya buge ni da gidin bindigar da yake dauke da shi, ya umurceni da kwanta a kasa”

“Haka kazalika suka yi ga ‘yan kabu-kabu biyun da ke tare da mu. Anan take suka harbe guda a yayin da yake kokarin guduwa, gudan kuma suka caka masa yuka har ga mutuwa don yayi kuwa” inji bayanin Rayyanu.