Connect with us

Uncategorized

Kalli yadda wani ya Mutu bayan ya Sace Gunkin kabilar ‘yan Tivi da ke a Jihar Taraba

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00
Naija News Hausa ta karbi rahoton mutuwar wani matashi da ya mutu bayan kwana uku da ya sace gunkin ‘yan kabilar Tiv da ke zaune a Jihar Taraba.
Bisa bayanin manema labarai, matashin ya haura ne zuwa shiyar ‘yan yaran Tiv da suka tare a yankin Jihar Taraba bayan farmaki da ya faru tsakanin Tiv da Jukun, daga isarsa da barazana sai ya sace gunkin na su.
An bayyana da cewa ko da ya sace gunkin bai gayawa ‘yan uwansa da suka tafi harin yankin ba. Da cewa ya tafi ne da gunkin har cikin dakin kwancin shi ya ajiye. Kamar yadda Mista Shamaki Solomon wani mazaunin Wukari ya bayar,  yace matashin ya kasa iya yin barci bayan da ya shigar da gunkin a cikin dakin sa.
Cikin gwagwar maya ne da hakan ya mutu bayan kwana uku.
Gunkin daman mutanen Tiv na amfani da shi ne don tsaron kansu a kauyan. Inji Mista Solomon,  “da mutumin ya gane da cewa ya kafa kansa cikin mawuyacin hali sai ya fara tone-tone da furta kalaman na tuba.”
“Na yi ta jin wata murya ne da karfi yana ikirarin cewa ‘Ina bukatar Jini, Ina bukatar Jini” inji Matashin da fadin cewa muryar na fita ne daga daki inda ya ajiye gunkin.
Ko da shike a lokacin da aka karbi rahoton, an bukaci samun bayani daga bakin kakakin yada yawun Jami’an tsaron Jihar Taraba, DSP David Misal, amma ya bayyana da cewa lallai hukumar su bata karbi wata sanarwa da hakan ba tukuna.