Connect with us

Uncategorized

‘Yan Hari da Bindiga a sabuwar hari sun kashe rayuka 34 a Jihar Zamfara

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Naija News Hausa ta karbi rahoto da cewa Mahara da Makami sun kashe akalla mutane 34 tsakanin kauyan Tungar Kafau da Gidan Wawa da ke a karamar hukumar Shinkafi, Jihar Zamfara.

An gane da shigar Mahara da Makamin ne akan babura, a missalin karfe biyar (5pm) na maraicen ranar Jumma’a da ta wuce, a inda suka fada wa mutanen kauyan da harbin bindiga ko ta ina da yiwa mutane raunuka.

Don bada tabbacin labarai, Kakakin yada yawu da sanarwa ga hukumar Jami’an tsaron Jihar Zamfara, Mista Mohammed Shehu, ya ce “Hukuma ta riga da sauwakar da yanayin tashin hankali a kauyukan, bayan mumunar hari da ‘yan hari da makami suka kai wa kauyan Tungar Kafau da Gidan wawa, inda suka kashe akalla mutane 34 a karamar hukumar Shibkafi”.

“Don hana da kuma magance irin wannan mumunar harin a Jihar Zamfara, Jami’an tsaron Jihar da da sauran hukumomin tsaro a Jihar sun hada kai don tabbatar da kadamar da sabbin hanyoyin tsaro ta musanman saboda samun zaman lafiya a shiyar.”

Mista Shehu, ya kara da cewa a ranar 15 ga watan Yuni 2019, kwamishanan hukumar tsaron Jihar Zamfara, CP Usman Nagogo, a jagorancin Gwamnann Jihar sun ziyarci kauyukan da harin ya faru don taya mutanen da bakin ciki da kuma kadamar da bizne mutanen da aka kashe a harin.

KARANTA WANNAN KUMA; Hukumar Tsaron Civil Defence Corps ta Jihar Imo sun gabatar da kame wani mutumi da ake kira Paul Ihuaku, da zargin kwanci da tsohuwar da ta haife shi.