Connect with us

Uncategorized

Kotun Koli ta Jihar Kano ta yanke wa wani hukunci Ratayar igiya har ga mutuwa (Karanta dalili)

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

A yau Talata, 18 ga watan Yuni 2019, Kotun Koli da ke a Jihar Yobe, ta gabatar da hukuncin ratayar igiya har ga mutuwa ga Muhammed Adamu, akan zargin kisan yarinyar da yake bida, Hauwa Muhammad mai shekaru 24 ga haifuwa.

Alkalin da ya gabatar da hukuncin, Mista A. Jauro ya bayyana da cewa Adamu ya karya dokar kasa da ke a falle na 221 cikin dokokin kasa.

“Akwai tabbaci da shaidu da ya nuna da cewa lallai saurayin ne ya kashe yarinyar shi Hausa” inji Jauro.

“A kan wannan, na yanke hukunci na gareka Muhammed Adamu, za a ratayaka ga igiya har sai ka mutu a rataye. Allah ya gafarta maka” inji Jauro.

Alkalin da ya tsaya wa Adamu a gaban kotun don neman yantarwa, Mista M. Dauda, ya fada da cewa zai wallafa sakon neman yanci da roko ga Kotun, wata kila ya samu yantar da Adamu.

Da aka nemi bayani daga bakin Adamu, saurayin da ya kashe yarinyar sa, sai yace “Na cika da du’a’i ga Allah don hukunci da ya fiye”

“Lallai na bada gaskiya ga nufin Allah a gareni, kuma na bada gaskiya ga duk matakin da ya bada daman a dauka ga hukuncin. Ina kuma a shirye da daukar kadara” inji shi Adamu.

Kamar yadda manema labaran NAN suka bayar, da cewa an kame Adamu ne tun ranar 5 ga watan Yuni a shekarar 2018 bayan da Jami’an tsaron Jihar Yobe suka sanar da zargin cewa saurayin ya kashe masoyiyar sa Hausa, a ranar 29 ga watan Mayu ta shekarar 2018 da ta gabata.

Ko da shike Naija News Hausa bata iya samu tabbaci da dalilin da ya sa Adamu ya kashe yarinyar, Hauwa.

Mun ruwaito a Naija News Hausa a baya cewa wani ya kashe Makwabcin sa a Jihar Neja da laifin Lalata da Matarsa.

“Ina da cikakken murna da dauke rayuwan Muhammadu, ina kuma a shirye don fuskantar shari’a akan yin hakan” inji shi mutumin da ya kashe makwabcin sa.

KARANTA WANNA KUMA; Wani ya Mutu bayan da ya Sace Gunkin kabilar ‘yan Tivi da ke a Jihar Taraba