Connect with us

Labaran Najeriya

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Talata, 18 ga Watan Yuni, Shekara ta 2019

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Talata, 18 ga Watan Yuni, 2019

1. Kotun Koli ta dauki mataki game da karar Adeleke da Oyetola

Bisa rahotannai, Naija News ta fahimta da cewa a ranar Litini da ta gabata, Kotun Koli ta kafa baki ga karar dan takara da ya dace da kujerar gwamnan Jihar Osun a zaben 2018.

Bayan zaman da Kotun ta yi a ranar Litini, 17 ga watan Yuni, an gabatar da daga hukuncin karar zuwa ranar 5 ga watan Yuli ta shekarar 2019, don kadamar da shari’a akan jayayyan da karar dan takara daga PDP a kujerar gwamna Jihar Osun, Ademola Adeleke game da rashin amince da zaben Jihar ta shekarar 2018 da ta gabata.

2. Jam’iyyar AA sun dakatar da dan takarar kujerar gwamnan Jihar, Uche Nwosu

Jam’iyyar Action Alliance (AA) sun sanar da dakatar da dan takaran su a kujerar gwamnan Jihar Imo, Mista Uche Nwosu.

Naija News Hausa na da sanin cewa Nwosu suruki ne ga tsohon gwamnan Jihar Imo, Sanata Rochas Okorocha, wanda yayi jayayya da hukumar INEC a baya akan hana shi takardan wakilci a gidan Majalisar Dattijai.

3. Kano Emirate: Ba wata umarnin Kotu da ya isa dakatar da binciken mu – inji Hukumar bincike da cin hanci da rashawa a Kano

Hukumar bincike akan cin hanci da rashawa ta Jihar Kano da ake kira Complaints and Anti-Corruption Commission, sun yi barazana da cewa ba wata umarnin kotu da ya isa dakatar da su akan gudanar da binciken su game da halin makirci da cin hanci da ya auku a Sarautar Jihar Kano.

Naija News Hausa ta samu wannan sanin ne bisa wata gabatarwa da aka bayar a bakin Ciyaman na Hukumar, Mista Muhuyi Magaji Rimi Gado, a ranar Litini, 17 ga watan Yuni da ta wuce.

4. Kotun Kara ta Jihar Legas ta gabatar da shari’a akan zaben kujerar gwamnan Jihar

A ranar Litini da ta wuce, bisa shari’ar Kotun Kara, Gwamnan Jihar Legas, Mista Babajide Sanwo-Olu ya kada dan adawan sa ga neman zaben kujerar gwamna a zaben 2019.

Naija News Hausa ta fahimta da cewa dan takara daga jam’iyar Alliance for Democracy (AD), Mista Owolabi Salis da dan takara daga jam’iyar Labour party, LP, Farfesa Ifagbemi Awamaridi, sun gabatar da karar rashin amincewa da nasarar Sanwo-Olu ne a baya, akan zaben 2019.

5. ‘Yan Kunar bakin Wake sun kashe akalla mutane 20 a Gidan Kallon wasannai da ke a Borno

Rundunar Sojojin Najeriya sun sanar da cewa fiye da mutane 20 wasu ‘yan kunar bakin wake suka kashe da tashin bam a wata gidan kallon wasa da ke a Konduga, nan Jihar Borno.

Bisa rahoton da aka bayar ga Naija News Hausa, An sanar da cewa kimanin mutane 30 suka samu raunuka daban-daban a harin.

6. Karya ne, ban gargadi Buhari da bada daman takaran shugabancin ga Iyamirai ba a shekarar 2023 – Sanata Lawan

Sabon shugaban Sanatocin Najeriya, Sanata Ahmed Lawan yayi gabatar da yin watsi da jita-jitan da ya mamaye layin yanar gizon nishadi da zancen cewa ya gargadi Jam’iyyar APC da shugaba Muhammadu Buhari da bayar da daman neman takaran shugaban kasar Najeriya a zaben shekarar 2023 ga Iyamirai.

“Bani bane da wannan zancen, Lawan da ya furta kalamar sakatare ne ga Jam’iyyar APC a Jihar Adamawa, kuma inda aka samu matsalar rashin fahimtar, sunan mu daya” inji Sanata Lawan.

7. Hukumar INEC ta rantse da bada aiki ga ‘yan bautan kasa da suka gudanar da ayukan su yadda ya dace

Hukumar Gudanar da Hidimar Zaben Najeriya (INEC) ta bayyana da cewa lallai suna da babban mataki na musanman ga duk dan bautan kasa, watau masu (NYSC) da suka dauki aikin su da muhinmanci da kuma tafiyar da shi da adalci har ga karshe a shekarar 2019.

Haka kazalika hukumar tayi alkawalin kyautata wa wadanda zasu hada hannu ga hidimar zaben Jihar Bayelsa da Jihar Kogi da za a yi a watan Nuwamba ta shekarar 2019.

8. Ba abin da ke tafiya daidai a kasar mu Najeriya, Peter Obi ya kalubalanci shugaba Buhari

Mataimaki da abokin takara ga Atiku Abubakar a zaben shugaban kasa ta shekarar 2019, mista Peter Obi na Jam’iyyar PDP ya kalubalanci shugabancin Muhammadu Buhari a fadin cewa ba abin da ke tafiya yadda ya dace a kasar.

A lokacin da Obi ke bada bayani ga manema labarai a birnin Legas, ya kalubalanci shugaba Buhari da bayyana rukunin shugabancin sa ga mulki a karo ta biyu.

9. INEC ta bayyana dalilin da ya sa ba zata iya rage yawar Jam’iyu ba

Hukumar gudanar da zaben kasar Najeriya, INEC, a wata zaman bincike da tattaunawa game da zaben kasa da aka yi a ranar Litini da ta gabata, sun bayyana da cewa sun kasa ga dama da kuma ikon iya rage yawar Jam’iyu da ake da su a Najeriya.

Naija News Hausa ta gane da wannan zancen ne bisa bayanin Mista Muhammed Haruna, Kwamishanan INEC na tarayyar Jihar Nasarawa, Kogi da Kwara.

Ka samu kari da cikakken Labaran Najeriya a shafin Hausa.NaijaNews.Com