Connect with us

Uncategorized

Mutane 3 sun Mutu a sabuwar harin Mahara da Bindiga a kauyan Unguwar Rimi, Jihar Kaduna

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Akalla mutane uku aka bada tabbacin mutuwar su a sabuwar hari da mahara da bindiga suka kai a kauyan Unguwar Rimi da ke a yankin Chawai, karamar hukumar Kauru, Jihar Kaduna.

Kakakin yada yawun Jami’an tsaron Jihar Kaduna, DSP Yakubu Sabo, ya bayyana ga manema labaran NAN a hadewar su a Kaduna, da cewa hukumar su na da tabbacin harin ‘yan hari da makamin, kamar yadda suka aiwatar, a ranar Litini, 17 ga watan Yuni da ta gabata, a missalin karfe biyu da rabi (2:25 pm).

A bayanin sa, DPO Jami’an Tsaron yankin, Kauri, ya karbi wata kirar gaugawa ne da cewa mahara da bindiga sun fada wa Unguwan Rimi da hari da harbe-harben bindiga ko ta ina.

“A cikin harbe-harben da suka yi ta yi ne suka kashe wani dan yaro mai suna Monday Yahaya (mai shekara 8 da haifuwa), da kuma Samson David (da shekaru 17) hade da Ashimile Danladi (dan shekaru 9)” inji shi.

Mun ruwaito a Naija News Hausa cewa ‘Yan Hari da Bindiga a sabuwar hari sun kashe rayuka 34 a Jihar Zamfara.

Mista Sabo ya kara da cewa lallai jami’an tsaro sun riga sun tafi wajen da abin ya faru, sun riga kuma da kwace gawaki da kuma tabbatar da kwanciyar hankali.