Connect with us

Labaran Najeriya

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Laraba, 19 ga Watan Yuni, Shekara ta 2019

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Laraba, 19 ga Watan Yuni, 2019

1. Buhari ya rattaba hannu sake tsarafa makarantan Fasaha

Shugaba Muhammadu Buhari, a ranar Talata da ta wuce, ya rattaba hannu ga bil na taimaka ga sake karfafa makarantu Jami’a ta fasaha, watau Federal Polytechnics Amendment bill da National Institute for Security Studies.

Naija News Hausa ta samu tabbacin hakan ne daga sanarwan mai wakilcin shugaba Buhari a zaman Gidan Majalisar Dattijai da Wakilai, Alhaji Umar El-Yakub, a ranar Talata, 18 ga watan Yuni nan birnin Tarayya, Abuja.

2. Hukumar INEC ta kwace takardan wakilcin gidan Majalisa daga dan Majalisar APC

Hukumar Gudanar da Hidimar Zaben kasar Najeriya, INEC ta sanar da kwace takardan yancin wakilci a gidan Majalisa da aka bayar a baya ga Mista Sina Akinwunmi.

Naija News Hausa ta fahimta da cewa INEC tayi hakan ne ga Akinwunmi, dan Majalisa a karkashin Jam’iyyar APC, bayan da aka gabatar da nasarar sa a hidimar zaben 9 ga watan Maris 2019 da ta gabata, don wakilcin yankin Okitipupa, Jihar Ondo.

3. Gwamnan Jihar Kwara ya dakatar da Kansiloli 16 har ga tsawon wata 6

A ranar Talata da ta gabata, Mista AbdulRahman AbdulRazaq, sabon Gwamnan Jihar Kwara ya dakatar da masu wakilcin yankunonin 16 a Jihar Kwara.

Naija News ta gane da cewa Gwamnan ya dauki matakin ne bisa hadin kai da amincewar Majalisar Jihar.

4. Rev Supo Ayokunle ya lashe kujerar shugabancin CAN a karo ta biyu

A ranar Talata, 19 ga watan Yuni da ta wuce, Hadaddiyar Kungiyar Kiristocin Najeriya (CAN), ta sake zaben Rev Supo Ayokunle a matsayin shugaban kungiyar a karo ta biyu kan jagoranci.

Gidan labaran nan tamu na da sanin cewa Mista Ayokunle ne shugaban tarayya kuma ga Nigerian Baptist Convention.

5. Shugaba Buhari ya gana da Gwamnonin Jam’iyyar APC a cikin Aso Rock

Gwamnonin da suka lashen zaben shekarar 2019 a karkashin Jam’iyyar APC, sun yi zaman ganawa ta kofa kulle da shugaba Muhammadu Buhari a ranar Talata.

An yi zaman ne a nan gidan Majalisar shugabancin kasa da ke a cikin Aso Rock Villa, Abuja, a missalin karfe 11.37am na safiyar ranar Talata, bayan bayyanar shugaba Buhari.

6. Zaben 2019: Tsohon shugaban INEC, Jega yayi bayani akan Na’urar ajiye sakamakon zabe

Farfesa Attahiru Jega, tsohon ciyaman na Hukumar gudanar da hidimar zaben Najeriya (INEC) ya bada haske ga yin watsi da zancen cewa shi ne ya furtar da hirar cewa hukumar INEC tayi amfani da na’urar kwamfuta don ajiye sakamakon zaben 2019.

Ka tuna da cewa an zargi tsohon shugaba hukumar da fadin cewa INEC tayi amfani da Na’urar kwamfuta wajen ajiye sakamakon zaben 2019.

7. Dalilin da ya sa ba zamu gabatar da kasafin dukiyar Buhari ba  – CCB

Hukumar Code of Conduct Bureau (CCB) sun gayawa Hukumar Harkokin Tattalin Arziki da bincike kadamarwa (SERAP) da cewa ba zasu iya gabatar da kasafin dukiyar shugaba Muhammadu Buhari ba a wannan lokacin.

Hukumar CCB ta fadi wannan ne don mayar da martani ga zancen hukumar SERAP na bukatar hukumar da gabatar da dukiyar da Buhari ke da ita kamar yadda shugabannai da gwamnoni suka gabatar tun shekarar 1999.

Ka samu kari da cikakken Labaran Najeriya a shafin Hausa.NaijaNews.Com