Connect with us

Uncategorized

Ciyamomin Jihar Kwara sun kai Gwamnan Jihar a Kotu

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Ciyamomi 16 da gwamnatin Jihar Kwara ta gabatar da tsigewa ‘yan kwanaki da suka shige sun yi karar Gwamnan Jihar, Abdulrahman AbdulRazaq da ‘yan Majalisar Jihar zuwa Kotu.

A bayanin Ciyamomin, sun bayyana da cewa matakin gwamna Abdulrahman Abdurasak na dakatar da su ba daidai bane; “Wannan ba a kan doka bane, kuma barnan lokaci ne kawai wanda kuma bamu amince da ita ba” inji su.

Ciyaman na Kungiyar Ciyamomin kananan hukumomin Najeriya, Mista Joshua Adekanye ya gabatar da cewa akwai wata doka a kotu da ya hana irin wannan mataki ga kowane gwamnati.

Mista Joshua ya kara da cewa abin ya zan mashi da mamaki ganin gwamnan Jihar da daukan irin wannan matakin, da sanin cewa bawai sun kai ga karshen wakilcin su ba, wanda bissa ranar rantsarwa da kuma doka sai watan Nuwamba a shekara ta gaba kamin su karshe wakilcinsu.

Ko da shike, magatakardan Gwamnan, Mista Rafiu Ajakaye ya bayar da cewa gwamnan ya dauki matakin ne bisa hadin kai da amincewar majalisar jihar.

Naija News Hausa ta fahimta da cewa majalisar jihar ne ta gabatar da dakatar da ciyamomin jihar ya ga tsawon watannai shidda har su kamala wata bincike makirci da cin hanci da rashawa na kudi kimanin naira Biliyan Talatin da Uku (N33b).

KARANTA WANNAN KUMA; ‘Yan Ta’adda sun yiwa Oshiomhole da wasu ‘yan Majalisa 14 duka a Jihar Edo