Connect with us

Labaran Najeriya

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Alhamis, 20 ga Watan Yuni, Shekara ta 2019

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Alhamis, 20 ga Watan Yuni, 2019

1. Buhari yayi bayani game da harin ‘yan ta’adda a Taraba

A ranar Laraba, 20 ga watan Yuni da ta gabata, Shugaba Muhammadu Buhari ya la’ane harin da ‘yan ta’adda suka kai a Kona, wata gari a yankin Jihar Taraba.

Shugaban ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya rattaba hannu, wadda aka bayar daga bakin Garba Shehu, mai yada labarai ga shugaban.

2. Otedola ya bada haske ga zancen sayar da Kamfanin Forte Oil

Babban masana’anci da Biloniya a Najeriya, Mista Femi Otedola, a ranar Laraba da ta wuce ya bayyanar da tabbacin cewa zai sayar da kashin sa 75% da ke a Kamfanin Forte Oil.

A wata sako da aka bayar ga manema labarai, masana’ancin ya bayyana cewa ya dauki matakin ne don kafa kai ga sasshen wutan lantarke.

3. Boko Haram sun hari Sojojin Najeriya da ke a Borno, da Kashe mutane 20

‘Yan ta’addan Boko Haram sun kai wata sabuwar hari a rukunin Sojojin Najeriya da ke a karamar hukumar Gajiram Nganzai, Jihar Borno, inda suka kashe Sojoji akalla 20 da kuma sace wasu da dama.

Bisa rahoton da manema labaran Breaking Times suka bayar, an bayyana da cewa ‘yan ta’addan sun fito ne daga shiyar Badu, wata kauye da ke kilomita 45km zuwa ga Gajiram, daga nan kuma suka haura ga

4. Shugaban Sanatocin Najeriyaa, Lawan ya nada sabbin ma’aikata

Mista Ahmad Lawan, shugaban Majalisar Dattijai ya amince da sake nadin Mista Olu Onemola a matsayin mai wakilcin sa wajen sanarwa a layin yanar gizo.

Naija News Hausa ta fahimta da cewa Onemola ma’aikaci ne ga tsohon shugaban Majalisar Dattijai, Sanata Bukola Saraki.

5. Kada ku rabar da kasar Najeriya, wasu rukuni sun kalubalanci Obasanjo da Jonathan

Rukunin wasu ‘yan Najeriya sun gargadi da kalubalantar tsohin shugaban kasar Najeriya biyu, Olusegun Obasanjo da Dakta Goodluck Jonathan, akan harin shugabancin Muhammadu Buhari.

Rukunin su fada da cewa ya kamata ne tsohin shugabannan su kasance da kokarin kafa zaman lafiya a kasar ba watsar da zumunci ba, kamar yadda suka kasa a shugabancin su duka.

6. Osinbajo yayi kuka game da Talauci a kasar Najeriya

Mataimakin shugaban kasar Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo ya bayyana irin bakin ciki da yake cike da shi akan yadda Talauci ke shugabancin yawancin ‘yan Najeriya.

“Wannan yanayi kan hana ni barci a kashin gaskiya” inji Osinbajo.

Osinbajo ya bayyana zancen ne a lokacin da yake wata gabatarwa a ranar Talata da ta wuce a birnin Legas a wata hidima a Makarantan Sana’a ta Harvard Business School (HBS).

7. An yi wa Oshiomhole tare da wasu duka a Jihar Edo

Wasu ‘yan ta’adda masu tada zama tsaye a Jihar Edo a ranar Talata da ta wuce sun hari Mista Seidu Oshiomhole, kani ga Ciyaman na Jam’iyyar APC na Tarayya, Adams Oshiomhole, anan cikin Benin, babban birnin Jihar.

Bincike ya nuna da cewa ganawar ‘yan majalisai 9 cikin ‘yan majalisa 24 da jihar ke da ita ne mafarin tanzomar da ‘yan ta’adda suka tayar.

8. Matan Ciyaman na NLC ta karbi yanci daga hannun Mahara a Taraba

Matan Ciyaman na Kungiyar Ma’aikata (NLC) ta Jihar Taraba, Malama Abigail Peter ta karbi yanci daga kangin ‘yan ta’adda bayan tsawon kwanaki shidda da aka sace ta.

Naija News Hausa ta karbi rahoton cewa an saketa ne a daren ranar Talata da ta wuce, bisa rahoton Channels Television.

9. Abin da Hukumar ASUP suka fada akan bil da shugaba Buhari ya rattaba hannu

Haddaiyar Kungiyar Malaman Makarantar Fasaha (ASUP), a ranar Laraba da ta wuce sun mayar da martani ga matakin da shugaba Muhammadu Buhari ya dauka na sanya hannu ga wata dokar kadamarwa da karfafa Makarantar Fasaha.

Naija News Hausa ta samu sanin cewa Kungiyar ASUP a ranar Laraba ta jinjina wa matakin shugaban Buhari.

Ka samu kari da cikkaken Labaran Najeriya a shafin Hausa.NaijaNews.Com