Connect with us

Labaran Najeriya

Shugaba Muhammadu Buhari ya nada sabon Darakta na Kamfanin NNPC

Published

on

Naija News ta karbi rahoton cewa shugaba Muhammadu Buhari ya gabatar da sabon Darakta na Kamfanin Man Fetur na Tarayyar Najeriya (NNPC).

An bayyana a rahoton da cewa Buhari ya nada Mista Mele Kolo Kyari a matsayin darakta da jagoran kamfanin Man Fetur na NNPC, don maye gurbin tsohon shugaban kamfanin, Dakta Maikanti Baru.

Bisa rahoton, sabon shugaban kamfanin da Buhari ya nada zai fara aikin sa ne a ranar 7 ga watan Yuli ta shekarar 2019.

Karin bayanai zasu biyo a baya…..