Connect with us

Uncategorized

Dalilin da yasa muke son mu haɓakar da Almajiranci a Najeriya – NSA

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00
Malamin Makarantar Arabi

Hukumar NSA ta bayyana zancen haɓakar da almajiranci a kasar Najeriya a wata taron manema labaran da aka yi game da sakamakon zaman tattaunawar majalisar tattalin arzikin kasa (NEC), wanda mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya jagoranta a fadar majalisa da ke a birnin tarayya, Abuja.

Gwamnatin tarayya na la’akari da haɓakar da tsarin Almajiranci don magance tashin hankali a kasar, in ji fadin shugaban Hukumar Tsaron kasa (NSA), Mista Babagana Monguno.

Monguno ya gabatar da hakan ne ga manema labarai da Insfekta Janar na Jami’an Tsaron kasar, Mohammed Adamu, Gwamna Adamawa, Ahmadu Fintri, Gwamnan Anambra, Willie Obiano tare da Gwamnan Jihar Ondo, Rotimi Akeredolu.

“Yana da matukar muhimmanci a haɓakar da irin wadanan kungiyar da ke gudana da yawace yawace akan batun neman ilimin da a karshe ba shi da kafuwar gaskiya a cikinta, sannan a ta bangaren a fara haifar da matsala da zai raunana jama’a da kasar gaba daya” inji Monguno.

“A ƙarshe, gwamnati za ta habakar da hidimar wannan Almajiranci ne domin ba za mu ci gaba da samun matsaloli a zaman al’umma ba, barin yara da yawace yawace, a karshe kuma bayan ‘yan shekaru zai su zama matsala ga al’umma.”

“Ba wai muna batu ko shirin cin mutuncin su ba ne ko muzunta masu, a’a ba haka bane. Abin da muke so mu yi shi ne hada kai tare da gwamnatocin jihohi don tabbatar da samar da Ilimin kyauta ga kowane yaro. Wannan haki ne ga kowane yaro, dukan yara sun cancanta da Ilimi idan har sun kasance ‘yan Najeriya. “

Naija News Hausa ta ruwaito a baya da cewa Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Ganduje ya gabatar da karatun kyauta a Jihar ga ‘yan Firamare da Sakandare.Ganduje ya bayyana da tabbaci cewa gwamnatin sa zata tabbatar da cewa fiye da Malam Makarantan Firamare da Sakandiri dubu talatin (30,000) sun samu kwakwaran karatu da takardun da ya dace a jagorancin sa.

“Ku tafi makaranta, Roko da yawace yawace ba al’adar Musulunci bane” inji Ganduje.