Connect with us

Uncategorized

Gwamnatin Jihar Taraba ta rage tsawon sa’o’in dokar ƙuntatawa a Jalingo

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Jihar Taraba bayan bincike da ganewa game da matsalar hari a Jihar, musanman harin Makiyaya Fulani a shiyar Kona, gwamnatin jihar tayi binbini da neman janye dokar ƙuntatawar da aka gabatar da jihar a kwanakin baya a Jalingo, babban birnin Jihar Taraba.

A yanzu gwamnatin Jihar ta gabatar da sake tsarafa lokacin dokar ƙuntatawar.

Bisa ganewar Naija News Hausa, dokar ƙuntatawar zai fara ne a yanzu daga karfe shidda (6PM) na maraice zuwa karfe shidda (6AM) na safiya, maimakon yadda take a da daga karfe Hudu (4pm) na maraice zuwa karfe shidda na safiya (6am).

An gabatar da hakan ne bayan ci gaba da aka samu wajen kwanciyar hankali da karfafar tsaro a Jihar.

Naija News ta samu tabbacin hakan ne a sanarwa da Mista Bala Dan Abu, babban mataimakin Gwamnan Jihar a layin sadarwa ta layin yanar gizo ya bayar da rattaba hannu.

Gwamnatin Jihar ta nuna godiya da jinjina wa hukumomin tsaron Jihar ga irin gwagwarmayan da jayaya da suka yi da mahara, barayi da ‘yan ta’adda a Jihar, da kuma tabbatar da zaman lafiya a Jihar.

An kuma roki mazaunan Jalingo duka da yin hankuri da bin dokar har sai komai ya lafa.

KARANTA WANNAN KUMA; Dalilin da yasa muke batun dakatar da Almajiranci a Najeriya – Gwamnati