Connect with us

Labaran Najeriya

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Litini, 24 ga Watan Yuni, Shekara ta 2019

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Litini, 24 ga Watan Yuni, 2019

1. Oshiomhole na bayyana Makirci – Obaseki

Gwamnan Jihar Edo, Gwamna Godwin Obaseki ya na zargin Ciyaman Tarayyar Jam’iyyar APC, Adams Oshiomhole da kadamar da makirci ga hidimar majalisar Jihar.

Naija News ta tuna da cewa a baya a wata taro, Oshiomhole ya kamanta matsalar Majalisar Jihar Edo da Majalisar Jihar Bauchi.

2. Tsohon Maa’ikaci ga Saraki yayi murabus da matsayin da Shugaban Sanatocin Najeriya ya bashi

Olu Onemola, tsohon ma’aikaci ga Bukola Saraki, tsohon shugaban sanatocin Najeriya, yayi rashin amincewa da matsayin babban mataimakin sadarwa a layin yanar gizo da Shugaban Majalisar Dattijai, Ahmed Lawan ya sanya shi.

Naija News Hausa na da sanin cewa matsayin ne Onemola ya rike a lokacin Bukola Saraki ke jagorancin Majalisar Dattijai kamin ya sauka daga kujerar.

3. Gwamnonin Jiha sun bukaci a musanya Oshiomhole, shugaban Jam’iyyar APC na Tarayya

Hagitsi a Jam’iyyar APC a yayin da mambobin Jam’iyyar a ranar Asabar, 22 ga watan Yuni da ta gabata, gwamnonin Jam’iyyar sun gabatar da zancen bukatar a tsige Adams Oshiomhole daga kujerar jagorancin Jam’iyyar.

Naija News Hausa ta gane da cewa tun karewar zaben shugaban kasa da zabunan da aka yi a watannai da suka shige, manya a jam’iyyar APC na gabatar da zargi da neman a musanya Oshiomhole a zaman Ciyaman na Jam’iyyar.

4. Jam’iyyar APC sun mayar da martani ga batun Hargitsi da ke faruwa a Majalisar Jihar Edo

Jam’iyyar Shugabanci, APC sun mayar da martani ga zancen Gwamnan Jihar Edo, Godwin Obaseki akan zargin da ya gabatar akan Ciyaman na Tarayyyar Jam’iyyar APC, Adams Oshiomhole, akan cewa yana kadamar da makirci ga hidimar majalisar Jihar.

Naija News ta fahimta a baya da cewa Obaseki ya zargi Ciyaman na Jam’iyyar da kasancewa da halin Makirci.

5. Jami’an tsaro sun gabatar da kimanin mutanen da suka mutu a fashewar wuta da ya faru a Rivers

Jami’an tsaron Jihar Rivers a ranar Asabar da ta wuce sun bada tabbacin kimanin mutanen da suka mutu sakamakon hadarin gobarar wuta da ya faru bayan da mabulbulin man fetur ya fashe a Jihar.

Wannan sanarwan ya biyo ne bayan da aka sanar da cewa gobarar wutan ya kori mazauna shiyar daga gidajen su.

6. Jami’an tsaro sun yiwa wani mutumi duuka

Wani matashi da aka gane da sunan sa a layin yanar gizon Facebook da Sagacious Louis, a ranar Jumma’a da ta wuce ya ci mugun duuka a hannun jami’an tsaron ‘yan sandan Najeriya da ke a jihar Delta.

Naija News Hausa ta fahimta da cewa hakan ya faru ne da matashin bayan da ya furtar da kalaman kokarin koyawa jami’an tsaron aikinsu.

7. Tsohon Minista ya bayyana lokacin da shugaba Buhari zai gabatar da Rukunin sa

Tsohon Minista a karkashin shugaban Shugaba Muhammadu Buhari, ya fada da cewa yana hangen cewa shugaban zai gabatar da jerin wadanda zasu kasance a rukunin shugabancin sa ga Majalisa a wata na gaba.

Tsohon Ministan ya bayyana ga manema labaran The Punch cewa Buhari na kokarin magance matsalar yin jinkiri a shirin gabatar da rukunin kamar yadda ya faru a baya.

8. Wata babban Gida ta rushe a Jihar Legas

A ranar Lahadi da ta gabata, wata gidan Sama mai tsani daya ta rushe a shiyar Oshodi, nan Jihar Legas, inda mutane biyu suka mutu.

Naija News ta samu tabbacin cewa abin ya faru ne gida da ke a lamba na 35, Adesanya Street, unguwar Mafoluku, a shiyar Oshodi.

9. Sananen Fasto ya gargadi shugaba Buhari akan rukunin sa a shugabanci na karo biyu

Babban Fasto da ke jagorancin Ikilisiyar The Awaiting The Second Coming Of Jesus Christ Gospel Church, Fasto Adewale Giwa ya gargadi shugaba Muhammadu Buhari da zaban masu adalci da kuma dacewa ga rukunin shugabancin sa a karo ta biyu.

A yayin da Faston ke bayaninsa a Akure, Jihar Ondo, ya shawarci Buhari da tabbatar da cewa mutanen da ke da gurin ci gaba da sadaukarwa ga kasar ne kawai zai sanya a rukunin sa.

Ka samu kari da cikakken Labaran Najeriya a shafin Hausa.NaijaNews.Com