Connect with us

Labaran Nishadi

Kalli yadda Gidan sama mai Tsani daya ya Rushe da mutane biyu a Jihar Legas

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Wata babban Gida ta rushe a Jihar Legas

Kamar yadda muka sanar a Naija News Hausa ‘yan sa’o’i da suka wuce a cikin Manyan Labaran Jaridun Najeriya ta ranar Litini da cewa, A ranar Lahadi da ta gabata, wata gidan Sama mai tsani daya ta rushe a shiyar Oshodi, nan Jihar Legas, inda mutane biyu suka mutu.

Naija News ta samu tabbacin cewa abin ya faru ne gida da ke a lamba na 35, Adesanya Street, unguwar Mafoluku, a shiyar Oshodi.

Bisa rahotannai, mutane da dama sun sami mugan raunuka da dama a rushewar ginin, bayan da aka bada tabbacin mutuwar mutum biyu.

Haka kazalika Hukumar LASEMA ta Jihar Legas a layin yanar gizon nishadi ta Twitter sun bada tabbacin mutuwar mutane biyu a take cikin gini, da cewa ginin ta rushe ne a yayin da ake wata gyarar da bai dace ba akan doka da sharadin gine-gine.

Karanta sakon hukumar a layin Twitter da hotuna a kasa;