Connect with us

Uncategorized

Dibi sabon Nasarar Sojojin Najeriya da Boko Haram a Jihar Borno

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Rundunar Sojojin Najeriya sun gabatar da yin nasara da karban yanci ga Mata 42, Maza 51 da ‘yan yara kanana biyu daga kangin ‘yan ta’addan Boko Haram a wata yawon zagaye da suka yi a Jihar Borno.

Naija News Hausa ta samu tabbacin hakan ne bisa bada tabbaci da Col. Sagir Musa, babban jami’in tsaron sadarwa ga rundunar sojojin ya bayar, inda ya bayyana da cewa sojojin sun ci nasara ga kashe ‘yan ta’adda Uku a zagayen.

An bayyana da cewa an gane ‘yan ta’addan Boko Haram din ne da yin amfani da mutane da suka katange wajen yin aikin gona da su.

Bisa bayanin Col. Sagir, rundunar sojojin ta bayar da maganin Polio ga yara 24 cikin yaran da aka ribato a zagayan.

Ya kara da cewa sun rushe sabbin rukunin wajen zaman da ‘yan ta’addan suka shirya a cikin dogon dajin. Bayan hakan kuma sun gano da wasu Qur’an, Janareto daya, Kekuna biyar, Tutoci, Layin wayar Salula biyar, da kuma kayakin sawa masu tsadar gaske.