Connect with us

Uncategorized

An kame wani tsoho a Jihar Bauchi da yiwa karamar yarinya mai shekara 11 Fyade dole

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Jami’an tsaro sun kame wani mutumi da aka bayyana sunan sa da Bashar Haruna, da zargin kwanci da wata karamar yarinya mai shekaru 11 ga haifuwa, a nan Jihar Bauchi.

Haka kazalika aka kame wani mutumi shima da tsawon shekaru 55 da zargin yiwa yarinyar da aka bayar da cewa ta saura aji na Hudu a karatun makarantar Firamare.

Naija News Hausa ta samu tabbacin rahoton ne bisa wata sanarwa da kakakin yada yawun Jami’an tsaron Bauchi, Mista Kamal Abubakar ya bayar ga manema labaran Northern City News a nan Bauchi.

Ka tuna mun ruwaito a Naija News Hausa a baya da cewa Hukumar Tsaron Civil Defence Corps ta Jihar Imo sun gabatar da kame wani mutumi da ake kira Paul Ihuaku, da zargin kwanci da tsohuwar da ta haife shi.

Mista Abubakar a bayanin sa ya fada da cewa “Tabas zancen da gaske ne, mun gane da kuma tabbatar da zargin. An gabatar ne da karar tun ranar 16 ga watan Yuni, 2019″ inji shi.

“Lallai mun karbi kira ne a ranar 16 ga watan Yuni, 2019, a missalin karfe 2 na tsakar ranar daga bakin wani mutumi mai suna Abubakar Haruna, mai shekara 43 ga haifuwa, mazaunin shiyar Sabuwar Kasuwa ta Bauchi”

“A bayanin Malam Abubakar, ya fada mana da cewa ya bar shagon sa ne a missalin karfe 10 na safiyar ranar zuwa gidansa, a isarsa a gida sai kwaram ya iske Bashar mai shekaru 25 kan ‘yar uwansa yana mata fyade”

Bisa karin bayanin Jami’in tsaron, Yarinyar ta bayyana garesu da wani mutumi mai suna Isah Sule, mazaunin Sabuwar Kasuwa, da suka kame a baya da zargin kwanci da yarinyar kuma sau da dama.

An bayyana da cewa ana kan karin bincike akan lamarin, za a kuma gabatar da su a kotu bayan bincike don daukan matakin da ya dace da su bisa doka.