Kalli yadda ‘yan Boko Haram suka yi wa wani Sojan Najeriya

Naija News Hausa ta gano da wani bidiyo da ke dauke da mugun yanayin da ‘yan ta’addan Boko Haram suka bar wani jarumin Sojan Najeriya a wata ganawar wuta da suka yi da rundunar Sojojin.

Ko da shike ba a bayyana inda hakan ya faru ba, amma a cikin bidiyon da aka rabar a layin yanar gizon nishadi ta Twitter daga hannun Reno Omokri,  tsohon ma’aikaci ga tsohon shugaban kasar Najeriya, Goodbluck Jonathan, zaka ga sojan cikin mawuyacin hali a yadda aka lallata masa kafafun sa da harbi.

“Kada ku raina kokari da gwagwarmayan rundunar tsaron Najeriya, musanman Sojoji” inji Reno Omokri.

Kalli bidiyon a kasa;

https://twitter.com/renoomokri/status/1143408811283288064