Uncategorized
Karanta dalilin da ya sa aka jefa wani Malamin Islamiyya a Kurkuku
An gabatar da wani mutumi mai suna Abdulsalam Salaudeen a gaban kotun kara ta Jihar Legas da zargin kwanci da wata karamar yarinya mai shekaru 5 ga haifufuwa.
Naija News Hausa bisa bincike da sanarwan rahotannai ta sami sanin cewa Abdulsalam Malamin Arabi ne, da tsawon shekaru 43 ga haifufwa.
An bayyana da cewa yakan koyar da yara ne a wata makarantar Islamiya da ke a shiyar Olorungbebe Mosque, Iyana Ile-Oba, yankin Igando ta jihar Legas, a inda ya ci amanan karamar yarinyar da kwanci da ita.
Manema labaran jaridar Punch sun bayar da cewa wani makwabcin Abdulsalam ne ya sanar da hakan ga Jami’an tsaro, bayan da ya dauki bidiyon Malamin ya kuma mikar da shi ga Jami’an tsaro don shaida ga zargin.
A bayan hakan ne Tsohon kwamishanan Jami’an tsaron Jihar, Mista Edgal Imohimi ya bada umurni ga darukan tsaro da su nemi Malamin, su kuma kame shi.
Rahoto ta nuna da cewa an rigaya da gabatar da karar Malam Salaudeen a kotu tun watannai da suka gabata a gaban Kotun Majitare ta Ikeja, ko da shike ya karyace zancen ba tare da sanin cewa makwabcin sa na da cikakken sani da mugun halin ba.
Alkali Soladoye da ke jagorancin karar ya bada umurnin cewa a katange Malamin a Gidan Yarin Kirikiri da ke a Legas, ya kuma daga karshen karar zuwa ranar 14 ga watan Aktoba ta gaba, kamin a dauki mataki na karshe a kasan Abdulsalam Salaudeen.
Mun ruwaito a Naija News Hausa a baya da cewa An kame wani tsoho a Jihar Bauchi da yiwa karamar yarinya mai shekara 11 Fyade dole.