Connect with us

Labaran Najeriya

APC/PDP: Kotun Kara taki amincewa da bukatar Atiku Abubakar don binciken Na’urar zaben 2019

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Bayan yawan gwagwarmaya da jaye-jaye, Kotun karar akan hidimar zaben kasa ta bayyana dagewa da kin bada dama ga dan takaran kujerar shugaban kasa daga jam’iyyar PDP ga zaben 2019, Alhaji Atiku Abubakar don binciken na’urar da hukumar INEC tayi amfani da shi wajen hidimar zaben watan ranar 23 ga watan Fabrairu da ta gabata.

Naija News Hausa ta gane da cewa Kotun tayi hakan ne bayan da hukumar INEC ta dage da cewa basu yi amfani da wata na’urar kwamfuta ba wajen ajiye sakamakon zaben 2019.

Ka tuna da cewa a baya, Jam’iyyar Adawa (PDP) da Atiku Abubakar sun gabatar da zargi a baya a gaban kotun neman yanci da cewa basu amince da sakamakon da hukumar gudanar da zaben kasar, INEC ta gabatar ba a zaben shugaban kasa ta ranar 23 ga watan Fabrairu.

A cikin karar zargin da PDP suka gabatar, Atiku ya bayyana da cewa ya fiye shugaba Muhammadu Buhari da yawar kuri’u bisa sakamakon da ke a cikin na’urar kwamfutan.

Kalli sakamakon zaben a kasa kamar yadda Atiku ya gabatar a karar; 

Dan takaran shugaban kasar daga Jam’iyyar PDP, Atiku ya bayyana da cewa yana da yawar kuri’u 18,356,732, a yayin da kuma Muhammadu Buhari ke da yawar kuri’u 16,741,430. Ma’ana bisa wannan sakamakon, Atiku ne ya lashe zaben shugaban kasa ta shekarar 2019.

Duk da hakan Alkali Mohammed Garba, Ciyaman ga rukunin Alkalai biyar da ke jagorancin karar, ya yi watsi da zancen da kuma kin bada daman bincike ga Atiku.

Naija News Hausa ta ruwaito a baya da cewa Sanatan da ya wakilci Jihar Kaduna a Majalisar Dattajai na takwas, Sanata Shehu Sani yayi kira da gargadin Arewa da su manta da zancen neman shugabancin kasar Najeriya daga Arewacin kasar a zaben shugaban kasa ta 2023 da ke a gaba.