Connect with us

Uncategorized

Mahara da Bindiga sun Harbe Matan Ciyaman na Bunza, Da Dan Sanda daya a Jihar Kebbi

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Wasu ‘yan hari da makami sun harbe matar Ciyaman na karamar hukumar Bunza, dan sanda da kuma memba na kungiyar ‘yan tsaro a garin Zogirma da ke karkashin Kebbi.

A halin yanzu sanarwa ya bayyana da cewa suna a babban asibitin Federal Medical Centre (FMC), Birnin Kebbi, inda  kula da lafiyar jikunan su.

Aliyu Usman, wani mazaunin kauyen Zogirma, ya shaida wa manema labarai da cewa lokacin da ‘yan fashin suka shiga cikin garin sai suka fara harbe-harben su, kamin dada kuma suka sace matar daga gidanta.

“A farko da suka fada a gidan ciyaman din, basu samu shiga kofar ba, sai suka harbe kofar sau da yawa kamin suka samu hanyar shiga suka dauki matarsa” inji Usman.

Ya kara da cewa wani dan sanda da wani memban kungiyar masu tsaron garin sun bi bayan ‘yan bindigar a ƙoƙarin ceto matar.

“Da ‘yan hari da makamin suka gane da hakan sai suka ci gaba da harbe-harbe, nan suka harbe matar, dan sandan da kuma dan bangar” in ji shi.

Naija News Hausa ta fahimta a sanarwa da manema labarai suka bayar cewa Babban Jami’in Kimiyyar Lafiya, Asibitin FMC, Dakta Hamzat Balarabe, ya ce cibiyar a gaggauce ta yi wa dan bangan aikin tiyata domin kokarin tsirar da rayuwansa.

“Muna kokarin hanzari da sauri a kan kafa kula ga matar kuma a yayin da ita ma ta sami raunuka da dama a wasu ɓangaren kirjinta,” inji Dakta Balarabe.

Alhaji Bello Zogirma, ciyaman da kuma mijin matar da aka harba, ya tabbatar da wannan lamarin ga manema labarai, ya ce “Maharan da makamin sun fado da hari ne a garin a miisalin karfe 1:40 na safiyar ranar Lahadi, kuma suka yita harbe-harbe don tsoratar da mazauna.”

“Maharan sun sace mata na da kuma wani mutumi a garin. Ko da shike dai ba wanda ya mutu a harin” inji shi.

Ya kuma kara bada haske da cewa lallai ‘yan hari da makamin basu ci nasara da wucewa da wadanda suka sace ba a yayin da hukumomin tsaron yankin Zogirma suka fita ganawar wuta da su.

KARANTA WANNAN KUMA; Gwamnatin Jihar Taraba ta rage tsawon sa’o’in dokar ƙuntatawa a Jalingo