Connect with us

Labaran Najeriya

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Talata, 25 ga Watan Yuni, Shekara ta 2019

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Talata, 25 ga Watan Yuni, 2019

1. Bankin Tarayyar Najeriya ta bayyanar da Ajanda na shekara 5

A ranar Litini da ta gabata, Bankin Tarayyar Najeriya (CBN) ta gabatar da Ajanda na tsawon shekaru biyar.

Naija News ta fahimta bisa bayanin Gwamnan Bankin Tarayyar Najeriya, mista Godwin Emefiele da cewa bankin Apex zata kafa kai ga tsarafa da kuma karfafar da bankunan kasuwanci a cikin shekaru biyar ta gaba.

2. Kotun Kara ta kaurace wa bukatar Atiku Abubakar

Bayan yawan gwagwarmaya da jaye-jaye, Kotun karar akan hidimar zaben kasa ta bayyana dagewa da kin bada dama ga dan takaran kujerar shugaban kasa daga jam’iyyar PDP ga zaben 2019, Alhaji Atiku Abubakar don binciken na’urar da hukumar INEC tayi amfani da shi wajen hidimar zaben watan ranar 23 ga watan Fabrairu da ta gabata.

Naija News Hausa ta gane da cewa Kotun tayi hakan ne bayan da hukumar INEC suka dage da cewa basu yi amfani da wata na’urar kwamfuta ba wajen ajiye sakamakon zaben 2019.

3. Kotu ta bada umarnin kame jagoran kamfanin Innosson

Kotun Koli da ke a birnin Legas ta sanar da umarnin kame Mista Innocent Chukwuma, shugaba da jagoran kamfanin kirar mota a Najeriya da aka sani da Innosson Nigeria Ltd CEO.

An sanar da hakan ne a wata sakon umarni da Alkali Ayokunle Faji ya bayar a ranar Litini, 24 ga watan Yuni da ta gabata.

4. Dole ne Abba Kyari ya wuce

‘Yan Najeriya sun mamaye birnin Tarayya, Abuja da zanga-zanga da barazanar cewa “Dole ne Abba Kyari ya wuce”, a turance “Abba Kyari Must Go”.

Naija News Hausa ta iya gane da cewa manya daga Jam’iyyar APC ne suka fita zanga-zangar da bukatan a tsige Abba Kyari, babban Jami’in tsaro ga shugaba Muhammadu Buhari.

5. Gwamnatin Tarayya ta kafa sabon rukunin SEC

Gwamnatin Tarayyar Najeriya a jagorancin shugaba Muhammadu Buhari a ranar Litini da ta wuce, ta gabatar da sabon rukunin Hukumar Tsaro da Kadamarwa (SEC).

Naija News ta tuna a baya cewa shugaba Buhari a shekarar 2015 da ta wuce, ya tsige Mista Peter Obi a matsayin Ciyaman na hukumar, bayan da tsohon shugaban kasar, Goodluck Jonathan ya sanya shi.

6. Kotun Karar Zabe ta amince da bukatar Buhari

Kotun Hukunci a kan hidimar zaben kasa ta bada dama da hadin kai ga bukatar da shugaba Muhammadu Buhari ya gabatar na gyara martani da ya ruwaito a baya ga tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, Atiku Abubakar da Jam’iyyar Adawa (PDP).

Wannan bukatar Buhari ya biyo ne bayan da Atiku da Jam’iyyar PDP suka gabatar da karar rashin amincewa da nasarar Buhari a matsayin shugaban kasa ga zaben 2019.

7. Ka kafa kai ga matsalar tsaro da ke a Jihar Kaduna – CAN ta gayawa El-Rufai

Hadaddiyar Kungiyar Kiristocin Najeriya, CAN ta gargadi gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Rufai da ya mayar da hankalinsa ga magance matsalar tsaro a jihar maimakon kokarin iko ga hidimar adinni da wa’azi.

Rukunin Addinin Kiristocin kasar sun gabatar da zancen ne ga manema labarai bayan da suka kamala wata ganawa.

8. Sojojin Najeriya sun ribato Mata 42, Maza 51 da yara biyu daga hannun Boko Haram

Rundunar Sojojin Najeriya sun gabatar da yin nasara da karban yanci ga Mata 42, Maza 51 da ‘yan yara kanana biyu daga kangin ‘yan ta’addan Boko Haram a wata yawon zagaye da suka yi a Jihar Borno.

Naija News Hausa ta samu tabbacin hakan ne bisa bada tabbaci da Col. Sagir Musa, babban jami’in tsaron sadarwa ga rundunar sojojin ya bayar, inda ya bayyana da cewa sojojin sun ci nasara ga kashe ‘yan ta’adda Uku a zagayen.

9. Hukumar NAHCON ta rage ga Kudin zuwa Hajj ta 2019 (Karanta ko nawa aka rage)

Hukumar Tafiya zuwa ga Hidimar Hajj ta Najeriya (NAHCON) tayi binbini akan kudin tafiya zuwa kasar Makka, ta kuma gabatar da rage tsadar kudaden da ake biya.

Naija News Hausa ta gane da hakan ne bisa sanarwan da kakakin hukumar NAHCON, Fatima Sanda Usara ta bayar akan hidimar tafiyar zuwa Hajj ta shekarar 2019.

Ka samu kari da cikakken Labaran Najeriya a shafin Hausa.NaijaNews.Com