Connect with us

Uncategorized

Farmaki ya Tashi tsakanin ‘yan Tiv da Jukuns a Jihar Taraba

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Farmaki ya tashi a ranar Talata, 25 ga watan Yuni da ta wuce tsakanin ‘yan Tiv da Jukuns a kauyan Rafinkada ta karamar hukumar Wukari, Jihar Taraba, inda aka bayyanar da mutuwar mutun 5 da konewar gidaje a sakamakon fadar.

Naija News ta fahimta da hakan ne bisa bayanin Mista Daniel Adidas, Ciyaman na ‘yan Kulawa da zamantakewar gidajen hukumar, a kan wayar salula ga kungiyar manema labaran Najeriya (NAN), a nan Jalingo.

Mista Daniel a cikin bayanin sa ya bayyana da cewa ‘yan hari da bindiga sanye da kakin sojoji sun fadawa kauyan Rafinkada ne da kone-kone gidaje da wuta.

“wani jami’in tsaro daga rundunar sojojin Najeruya ya sami raunuka da dama a harin, kuma an kai shi a wata asibiti do bashi kulawa a Wukari” inji shi.

Haka kazalika DSP David Missal, kakakin yada yawun jami’an tsaron ‘yan sandan jihar, ya bada tabbacin farmakin da kuma mutuwar mutum guda.

“Bisa rahoton da aka isar a gaba na, na samun sanin cewa wasu matasa ‘yan hari daga Jihar Benue sun fada wa karamar hukumar Wukari a Jihar Taraba da fada, da kuma kone gidajen su” inji Missal.

Mun ruwaito a Naija News Hausa a baya da cewa ‘yan ta’addan Boko Haram sunyi wa wani matashi, jarumin Sojan Najeriya mumunar raunanawa da cin mutunci a wata ganawar wuta da suka yi.