Connect with us

Labaran Najeriya

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Laraba, 26 ga Watan Yuni, Shekara ta 2019

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Laraba, 26 ga Watan Yuni, 2019

1. INEC: ‘Yan Takaran Shugaban Kasa Sitin sun yi watsi da zancen Atiku da Jam’iyyar PDP

‘Yan takaran kujerar shugaban kasa Sitin (60) daga jam’iyu daban daban sun yi watsi da kuma kalubalantar dan takaran shugaban kasa daga jam’iyyar Adawa (PDP) a zaben 2019, Atiku Abubakar.

Naija News Hausa ta gane da cewa ‘yan takaran sun nuna rashin amincewa da zargin Atiku ne akan cewa Hukumar INEC tayi amfani da na’urar kwamfuta wajen shirya da ajiye sakamakon zaben watan Fabrairu.

2. Hukumar INEC na da yancin tsige kowace Jam’iya da suka ga dama – Ekweremadu

Mataimakin shugaban gidan Majalisar Dattijai na Takwas, Ike Ekweremadu ya bayyana da cewa dokoki da gidan majalisa ta da ta gabatar ya bada damar iya rage yawar jam’iyun takaran zabe a kasar.

Sanatan da ke wakilcin wata yanki a Jihar Enugu ya bayyana zancen ne a wata sanarwa da aka bayar daga bakin mai wakilcin sa ga sadarwa ta layin yanar gizo, Uche Anichukwu.

3. Kada ku cika da Murna tukuna  – Atiku ya kalubalanci shugabanci Najeriya

Tun da Kotun karar hidimar zaben kasa ta gabatar da hukuncin hana dan takaran kujerar shugaban kasa daga jam’iyyar PDP ga zaben 2019, Alhaji Atiku Abubakar binciken na’urar da hukumar INEC tayi amfani da shi wajen hidimar zaben watan ranar 23 ga watan Fabrairu da ta gabata, manyan ‘yan siyasa da ‘yan takara sun shiga yada yawun su ga Atiku da Jam’iyyar PDP.

Atiku Abubakar ya kalubalanci shugabancin kasar da cewa kada su fara rawa da tsalle-tsalle tukuna, da cewa “ba nan take ba an danne wa buddari kai.”

4. Shugaba Buhari ya bada tabbacin cika alkawali ga ‘yan Najeriya

Shugaban Muhammadu Buhari ya kara bada tabbaci ga al’ummar Najeriya da cewa kada su cika da damuwa a yayin da gwamnatinsa a wannan karo ta biyu zata cika dukan alkawalai da tayi ga kasar.

A bayanin shugaban, ya kara bada tabbacin hakan, musanman ga magance matsalar tsaro, samar da ci gaba ga kasar da zaman lafiya.

5. Dapo Abiodun yayi nasara a hukuncin kotu

Gwamnan Jihar Ogun, Dapo Abiodun yaci nasara ga karar kotu mai lamba No SC/524/2019 da Abdulrafiu Baruwa ya gabatar da zargin cewa bai dace da takara ba a Jihar.

Bisa rahotannai, Baruwa ya gabatar da karar ne da zargin cewa Gwamna Dapo bai bayyana dukan takardun makarantar sa ba ga neman zabe.

6. Zaben 2019: Ba zaben da ya zama cikakke a tarihi – inji shugaban hukumar INEC

Shugaban hukumar gudanar da hidimar zaben kasar Najeriya (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu ya dage da kare adalcin hukumar INEC ga hidimar zaben 2019 da aka kamala a baya.

Yakubu yayi hakan da fadin cewa a tarihance ba zaben da ya cika kashi 100% da kwarewa.

7. Shugaban Majalisar Dattijai, Lawan yayi bayani game da Albashin Sanatoci

Dakta Ahmad Lawan, shugaban sanatocin Najeriya ya karyace zancen jita-jita da ake na cewar majalisar nada wata shiri don kara ga albashin ‘yan majalisai.

Lawan ya karyace zancen ne a ranar Talata da ta gabata a wata ziyara da manya daga rukunin majalisar suka ziyarce shi, anan cikin Ofishin sa.

8. Kungiyar Afenifere sun kalubalanci Osinbajo akan zancen matsalar tsaro a Najeriya

Kungiyar Hadin Kai ta kasar Yarbawa, da aka fi sani da likin suna ‘Afenifere’ sun kalubalanci mataimakin shugaban kasar Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo, akan furcin da yayi na cewa karin ikirarin da ‘yan Najeriya ke yi akan matsalar tsaro a kasar Najeriya ba gaskiya bane.

Kungiyar, a bakin jagoransu Reuben Fasoranti, sun bayyana rashin jin dadi da amince da zancen Osinbajo, a bayanin sa da yayi ranar Lahadi da ta gabata a birnin New York.

9. Na Ari kudi Biliyan 7 don biyan Ma’aikata – Gwamna Abiodun

Gwamnan Jihar Ogun, Dapo Abiodun ya bayyana irin yanayi da ya iske asusun jihar a lokacin da ya karbi jagorancin jihar.

Gwamnan ya gabatar a bayaninsa da cewa sai da ya ari kudi kimanin naira Biliyan 7 don biyan albashin ma’aikata a Jihar.

Ka samu kari da cikakken Labaran Najeriya a shafin Hausa.NaijaNews.Com