Connect with us

Uncategorized

Kalli abinda Shugaban Majalisar Dattijai, Lawan ya fada game da Albashin ‘yan Majalisai

Published

on

Shugaban Majalisar Dattijai, Dokta Ahmad Lawan, ya ce babu wani wata kari ko albashin boye ga ‘yan majalisar dokokin kasar kamar yadda aka zayyana a wasu sassa.

Lawan ya gabatar da wannan bayanin ne a yayin da mambobin Majalisar Dattijai suka kai masa ziyara a ofishinsa a birnin Abuja ranar Talata.

A yayinda yake cikin bayanin da ba da la’akari ga zancen kudin kari a boye da ake zargin majalisar da ita, ya bayyana cewa albashin sa da ta kowane dan majalisar bai wuce N750,000 ba.

“Abin da nake so in jaddada a nan shi ne cewa ban taɓa yin imanin cewa akwai wani abu a Majalisar Dattijai da ake kira albashin Jombo (kari/boye) ba”

“A Majalisar Dokoki da Wakilai, kowa na karban daidai albashin sa ne, ni kuma ina karbar Naira Miliyan Dari Bakwai da Hamsin (N750,000) ne a matsayin albashi na.

“Amma dole ne inyi aiki a matsayin Sanata, ya kuma dace Ofishi na ya sami kulawa da ta dace” inji shi.

Sanata Lawan ya kuma yi alkawarin cewa Majalisar zata kasance a bude ga kowa don cin nasara a halartar da ayyukan majalissar, musamman ma a bangaren kudade.

KARANTA WANNAN KUMA;  Hukumar NAHCON ta rage ga Kudin zuwa Hajj ta 2019