Uncategorized
Ganduje yayi nadin sabon Sarauta a Jihar Kano
Gwamnan Jihar Kano, Gwamna Abdullahi Ganduje ya nada Ali Makoda a matsayin ‘Chief of Staff’ (Babban Jami’in Kadamar da Tsari a Jihar).
A ganewar Naija News Hausa, Makoda a shafin Ilimin Kimiya ya, yana da rikon digiri na B.A. a sashin Library/Political Science, da kuma Postgraduate Diploma in Management da Masters in Business Administration (MBA), daga Makarantar Bayero University, Kano.
Haka kazalika a baya yayi rikon matsayin Kwamishanan Muhali.
An sanar da nadin Makoda ne a wata gabatar wa da aka rattaba hannu da sanar a jagorancin babban sakataren gwamnan Jihar, Abba Anwar, a birnin Kano, yau Alhamis, 27 ga watan Yuni 2019.
“Ali Haruna Makoda mutun ne mai daraja ga jiharmu kwarai da gaske. Saboda haka ya kamata a daraja shi da kuma tabbatar da cewa ya kasance a rukunin jagoranci na ta karo biyu a ofishi” inji Ganduje.
KARANTA WANNAN KUMA; Arewa Ku Manta da zancen neman Shugabanci a Shekarar 2023 – inji Shehu Sani