Connect with us

Uncategorized

Gidan Sama mai Tsani Uku ya rushe da Mutane ciki a Jihar Legas (Kalli hotuna)

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Naija News Hausa ta karbi rahoton yadda wata gidan sama mai jeri Uku ya rushe da mutane 12 da raunuka a Jihar Legas.

Bisa rahoton da aka bayar ga manema labarai, hakan ya faru ne a daren ranar Laraba da ta gabata a shiyar Fagba, a Jihar Legas.

Babban Ofisan Hukumar Kulawar Gaggawa ta Jihar Legas (LASEMA), Dokta Olufemi Oke-Osanyintolu, ya kara bada haske ga alamarin, da fadin cewa “Ina sanar da tabbatar maku da rushewar gidan sama mai tsani Uku a nan shiyar K Farm, Fagba, hanyar da ta zagaya bawan Iju”

Ya kara da cewa lallai ana kan aiki ne a gidan a yayin da ya rushe da mutane ciki. Ko da shike ya bayyana da cewa mutanen da suka sami raunuka na karban kulawa a wata asibitin da ke a shiyar.

Naija News Hausa ta ruwaito a baya da rushewar wata gidan sama ta rushe a Jihar Legas

Ko da shike a gidan sama mai tsani ukun, ba rahoton cewa ko kila wani ya mutu a rushewar gidan, amma da tabbacin mutane goma shabiyu da raunuka.

“Za a karkare rushe dukan banaren ginin da ya saura tsaye don hanna shi fadowa ba daidai ba da kuma magance matsalar kara wata mumunar faduwa” inji Dokta Olufemi.

KARANTA WANNAN KUMA; Dalilin da ya sa aka jefa wani Malamin Islamiyya a Kurkuku